✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi damfarar Naira miliyan 360 daga cikin kurkukun Kirikiri

Ana binciken wani matashi da ke tsare a kurukukun kare kukanka na Kirikiri da ke Legas, kan zarginsa da yin damfarar Dala miliyan daya (kimanin…

Ana binciken wani matashi da ke tsare a kurukukun kare kukanka na Kirikiri da ke Legas, kan zarginsa da yin damfarar Dala miliyan daya (kimanin Naira miliyan 360), a lokacin da yake tsare a wannan kurukuku mafi tsananin tsaro a kasar nan.

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun ce wanda ake zargin mai suna Hope Olusegun Aroke ya yi amfani da gungun abokansa ne don yin wannan damfarar daga inda yake tsare a kurukukun.

An kama Hope Olusegun Aroke ne a shekarar 2012 inda aka yanke masa hukuncin dauri na shekara 24 kuma tun lokacin ya fara zaman sarka na shekara 24 a gidan kurukukun na Kirikiri.

Amma wani binciken farko-farko da aka gudanar ya gano cewa yana amfani da Intanet a gidan Kurukukun, wanda hakan ya ba shi damar aikata abin da ake zarginsa.

Wata sanarwa da Hukumar EFCC ta fitar a ranar Talata, ta ce ta samu wasu bayanan sirrri a kan damfarar da ake zargin Olusegun Aroke ya yi, kuma suna bincike kan yadda aka yi ya samu damar ci gaba da wannan “mummunar ta’asa” daga cikin gidan kurukukun.

Bayan da aka kama shi a shekarar 2012, Hukumar EFCC ta ce Aroke wanda tsohon dalibi ne a kasar Malaysiya, “shi ne kashin bayan duk wata damfara ta Intanet da ake yi a tsakanin kasashen Najeriya da Malaysiya,” kamar yadda Sashin Hausa na gidan rediyon BBC ya ruwaito.

A wannan mako ne Hukumar EFCC ta ce bincikenta na farko-farko ya gano cewa, “Aroke ya samu damar amfani da Intanet da kuma wayarsa, sabanin yadda doka ta tanada.”

An kuma kwantar da shi a wani Asibitin ’Yan sanda da ke Legas don duba lafiyarsa, inda daga can ya samu damar barin wajen ya koma yana zama a otel-otel, yana ganawa da matarsa da ’ya’yansa, har ma yana halartar tarurruka.