✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi wa mahaifiyarsa da surukarsa fyade

Wani matashi dan shekara 32 mai suna Dabid Shekari ya yi wa mahaifiyarsa da sukarsa fyadeya kauyen Reinden da ke Karamar Hukumar Kaura ta jihar…

Wani matashi dan shekara 32 mai suna Dabid Shekari ya yi wa mahaifiyarsa da sukarsa fyadeya kauyen Reinden da ke Karamar Hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Matashin wanda ya dade yana yi wa mata, musamman tsofaffi fyade ya fada komar ‘yan sanda, bayan labarinsa ya kai ga runduna ta musamman da ke kula da kai dauki, inda ta yi awon gaba da shi kuma ta ce dama tuni ta dade tana nemansa kan karin wasu laifuffuka daban da su ka hada da fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane.

A lokacin da ya ke yi wa ‘yan sanda bayani kan abinda ya sa ya ke aikata wannan mummunan aikin bayan ya amsa laifinsa, ya dora laifin hakan ga shaye-shaye inda ya ce sau biyu yana yi wa mahaifiyarsa mai shekara 65 fyade a tsakiyar dare.

“Ba na sanin halin da na ke ciki a duk lokacin da na sha barasa. Ni manomi ne kuma ina da mata daya amma ta guje ni saboda wannan dabi’ar ta yi wa tsofaffi fyade. Duk lokacin da na bugu na kan rasa abin da ya ke min dadi a duniya face in ga na yi wa tsofaffin mata fyade. An sha kama ni ana min duka amma kamar asiri har yanzu na kasa dainawa.

“Na yi wa mahaifiyata fyade ne wata rana bayan na dawo bikin gargajiyarmu na Moroha da mu ke yi. Bayan na bugu na yi ta neman matan da zan yi wa fyade ban samu ba, a haka har na isa gida. Ina zuwa gida na tarar da mahaifiyata a kwance tana barci shi ne na afka mata,” inji shi.

Dabid ya ce mahaifiyarsa ta yi ta ihu yayin da ta gan shi, amma daga baya ya roke ta gafara wanda a sandiyyar wannan aika-aikar ne matarsa ta gudu ta koma kauyensu Mahuta ta sake yin wani aure a can.

Amma bayan guduwarta, watarana ya tafi kauyen da matarsa ta ke don halartar wani bikin sai ya sake shan kayan maye inda ya bugu kuma nan da nan, kamar yadda ya saba sai fara neman wacce zai yi wa fyade, inda nan take ya afka gidan surukarsa a lokacin da ta ke barci. Sai dai dubunsa ta cika bayan ta kwarma ihu yayin da ta bude ido ta gan shi, inda aka lakada masa dukan tsiya.

Rundunar ‘Yan Sanda ta ce ta cafke shi ne tare da taimakon wasu ‘yan sintiri a wata maboyarsa a garin Manchok inda aka kama shi tare da babur din da ya yi kwacenta inda a yanzu haka ya ke tsare a hannunsu.

Wadanda Aminiya ta tuntuba a kauyukan guda biyu sun ki cewa komai a kai, sai wani da ya bukaci a sakaye sunansa da ya ce wannan labarin shekararre ne don ya faru ne tun shekarar 2017 kuma tun lokacin ya ke hannun ‘yan sanda. Idan aka same shi da laifin da ake tuhumarsa zai fuskanci hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari inji wani dan sanda.