Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Matashi ya yi wa ‘yar shekara biyar fyade.

Chinonso Ugochukwu

Matashi ya yi wa ‘yar shekara biyar fyade.

’Yan sanda sun damke wani matashi mai shekara 28 da ya lalata wata ’yar shekara biyar a unguwar  Ndikokwu Umuaku Uli da ke Karamar Hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Anambara SP Haruna Mohammed ya ce matashin ya shigar da yarin dakinsa ne ya yi mata fyade.

“Mun kama matashin …kan zargin yin lalata da wata karamar yarinya.”

Sanarwar da ’yan sandan suka fitar ta ce matashin wanda aka fi sani da suna NEPA na nan a tsare yayin da aka kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar CP John B. Abang ya umarci sashen binciken manyan laifuka rundunar ya ci cikakken bincike kan fyaden kafin a gurfanar da matashin a kotu.