✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya zama Shugaban Majalisar Jihar Oyo

Sabon Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya kaddamar da sabuwar Majalisar Dokokin Jihar ta 9 tare da yin kira ga wakilan majalisar su jingine…

Sabon Gwamnan Jihar Oyo Injiniya Seyi Makinde ya kaddamar da sabuwar Majalisar Dokokin Jihar ta 9 tare da yin kira ga wakilan majalisar su jingine bambancin siyasa waje daya su hada kai da bangaren zartarwa domin yin aikin ci gaba ga jama’ar da suka zabe su. Gwamnan wanda ya kaddamar da majalisar a ranar Litinin da ta gabata, ya ce Jihar Oyo ba za ta taba ci gaba ba muddin babu hadin kai a tsakanin bangarorin biyu.

Jim kadan bayan kaddamarwar ce wakilan majalisar suka zabi Mista Adebo Ogundoyin wanda matashi ne dan shekara 32 a matsayin sabon Shugaban Majalisar. Wakilai 32 na majalisar ce suka zabi Adebo Ogundoyin ba tare da hamayya ba. Wannan shi ne karo na farko da aka zabi shugaban majalisar mai karancin shekaru a jihar.

Mista Adebo Ogundoyin yana daga cikin wakilan tsohuwar majalisar ta 8 da ya yi nasarar lashe zabe a karkashin Jam’iyyar PDP a Mazabar Ibarapa ta Gabas a zaben cike gurbi da aka yi a bara bayan rasuwar Shugaban Majalisar Mista Michael Adeyemo a cikin watan Afrilun bara.

Ogundoyin ya sake nasarar lashe zaben wannan kujera a zaben 9 ga Maris na bana inda da ya kai shi ga zama sabon shugaban majalisar ta 9.

A daidai lokacin ne wakilan majalisar suka zabi Mista Abiodun Fadeyi daga Mazabar Ona Ara a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar da Onaolapo Sanjo daga Mazabar Ogbomoso ta Kudu a matsayin Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakinsa Olasunkanmi Babalola daga Mazabar Egbeda tare da Asimiyu Alarape daga Mazabar Atiba a matsayin Shugaban Marasa Rinjaye da dukkansu sun sha rantsuwa a gaban Gwamna da Mataimakinsa da kuma sarakuna da sauran baki.