Aminiya

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin “Divine church of God” a yankin Ejigbo a Legas ya shiga komar ‘yan sanda bayan da ya fasa akwatin ajiyar kudin cocin inda ya sace kudin.

A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, a ranar 30 ga watan da ya gabata  faston cocin Moses Nwoke, ne ya  shigar da karar a ofishin ‘yan sandan yankin Ejigbo, inda suka shaida cewa, an shiga cocin an kwashe kudin sadaka  da mabiya cocin suka bayar aka boye su a wani akwatu, “Daga nan ne muka kaddamar da bincike muka kame matashin mai shekaru 18 mai suna  Elikor Ehud, da ya tabbatar mana da cewa shi ya fasa akwatin ya sace kudin Naira dubu 670, ya ce ya yi hakan ne tare da taimakon wani abokin ta’asar sa wanda zuwa yanzu ake nema ruwa a jallo.” In ji shi.

ADVERTISEMENT

Ya ce, za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

ADVERTISEMENT