✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin dan kwallon Ingila ya amince ya wakilci Njeriya

Matashin dan wasan Ingila wanda asalinsa dan Najeriya ne, Lookman Ademole ya amince ya ajiye kasar Ingila domin ya wakilci Najeriya. Dan wasan ya wakilci…

Matashin dan wasan Ingila wanda asalinsa dan Najeriya ne, Lookman Ademole ya amince ya ajiye kasar Ingila domin ya wakilci Najeriya.

Dan wasan ya wakilci Ingila mai shekara 22 ya wakilci Ingila a gasar ’yan kasa da shekara 17 da 20, inda ya lashe Kofin Duniya a shekarar 2017.

Ya fara fitowa ne a kungiyar Everton ta Ingila, inda ya fara buga Gasar Firimiya, sannan daga bisani aka tura shi aro a kungiyar RB Leopzig a kakar bara, inda ya zura kwallo 5 a wasa 11.

Wannan ne ya sa kungiyar da ke wasa a Gasar Bundesliga ta Jamus, ta saye shi a farkon kakar bana.

Duk da cewa dai ya wakilci Ingila, dokar Hukumar FIFA ta ba shi dama ya sauya sheka matukar bai wakilci kasar Ingila a matakin manya ba.

Mataimaki wajen horar da ’yan wasa a Hukumar NFF, Tunde Adelakun ne ya tabbatar da hakan.