Da Dumi Dumi

Matattu 596 ake biyansu albashi a Bauchi

Gwamna Jihar Bauchi Bala Mohammed
Gwamna Jihar Bauchi Bala Mohammed

Kwamitin da Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar  don binciken ma’aikatan da basu da lambar Tantance Asusun Banki ta BVN ya bankado wasu matattun ma’aikata 596 da ake biyansu albashi.

Akalla ma’aikata dubu 4,578 da ‘yan fansho ne suka ki halartar tantancewar kwamitin saboda lambar BVN . Shugaban Kwamitin Adamu Ibrahim Gumba, ne sanar da hakan ga manema labarai.

Adamu Ibrahim, ya kara da cewa kwamitin ya bai wa ma’aikatan dama don tantance su da sauran masu karbar fansho, amma suka yi watsi da wannan damar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya