✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsafa sun kashe daliba bayan sun yi mata fyade

An kashe wata dalibar kwaleji da aka sassara da adda bayan an yi mata fyade a cikin coci. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta ce…

An kashe wata dalibar kwaleji da aka sassara da adda bayan an yi mata fyade a cikin coci.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta ce Grace Oshiagwu ta rasu ne bayan matsfan sun yi mata fyade sun kuma sassare ta.

Aminiya ta ruwaito cewa aika-aikan na zuwa ne kimanin makonni biyu da aka yi wa wata budurwa mai suna Barakat Bello fyade aka aka kuma kashe ta a yankin.

A karamar Hukumar ta Akinyele ce kuma aka yi wa wata mata mai juna biyu da ke karatu a jami’a fyade aka kuma kashe ta.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo Olugbenga Fadeyi, ya kara da cewa, “Mun fara gudanar da bincike da kokarin gano miyagun domin a hukunta su.

“Muna rokon duk mai wani kwakkaran bayani da ya taimaka domin mu magance wannan danyen aiki”, inji shi