Matsafa sun kwakule idanun wani yaro a Nasarawa

Wadansu da ake zargin matsafa ne sun kai hari a kauyen Agaza da ke Karamar Hukumar Keana a Jihar Nasarawa, inda suka sace wani karamin yaro mai suna Monday Agadi, daga bisani kuma suka kwakule idanunsa.

Wakilinmu ya ziyarci kauyen da lamarin ya auku, inda ya zanta da mahaifin yaron mai suna Agadi Ajeh wanda ya ce matsafan sun iso gidansa ne da misalin karfe 1:00 na dare lokacin shi da iyalansa suna barci suka sace yaron.

Ya ce “Da gari ya waye ba mu ji duriyar yaronmu ba ne sai muka fara nemansa, daga bisani muka samu labarin cewa an cire wa wani karamin yaro ido a wani daji, kuma da muka je sai muka tarar danmu  ne. Daga nan sai muka garzaya da shi wani karamin asibiti a kusa da mu, daga bisani muka wuce da shi zuwa Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya, sannan muka sanar da ’yan sanda faruwar lamarin,” inji shi.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Usman Isma’ila dangane da aukuwar lamarin, inda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma bayyana cewa bincike da jami’ansa suka gudanar sun gano cewa kafin aukuwar lamarin yaron ya yi ta sanar da iyayensa cewa akwai wadansu mutane da suke ta yi masa barazana cewa za su cire masa idanu, amma iyayen  ba su kula da shi ba.

Ya ce, “Ka ga yaron da lamarin ya shafa bincikenmu ya gano cewa ya yi ta sanar da iyayensa cewa wadansu suna yi masa barazanar cewa za su sace shi su cire masa idanu, amma iyayen nasa ba su dauki maganar da muhimmanci ba. Kuma ba su sanar da ’yan sanda ba, kuma bayan wasu kwanaki ne wadansu miyagun mutane da ba a san ko su wane ne ba suka sace shi zuwa wani daji da ya kai nisan kilomita biyu daga kauyen, suka cire idonsa suka bar shi a dajin. Washegari ne iyayen yaron suka sanar da jami’anmu da ke ofishinmu na Keana. Amma a halin yanzu muna ci gaba da bincike har sai mun gano wadannan miyagun mutane da suka aikata danyen aikin, don gurfanar da su a gaban kotu su fuskanci hukunci.”

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa “Saboda haka ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga iyayen yara, su rika sa ido a kan ’ya’yansu kasancewa bikin Kirstimeti yana gabatowa, miyagun mutane suna fadada ayyukansu a yanzu, kuma a rika sanar da jami’anmu da sauran hukumomin tsaro a kan lokaci a duk lokaci da irin wannan abu ya auku domin ba mu damar gudanar da aikinmu yadda ya kamata ba sai lamarin ya yi muni a sanar da mu ba.”

A halin da ake ciki dai karamin yaron da lamarin ya shafa yana  jinya a Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya fadar jihar.

 

Share