✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsafa sun sare hannun magidanci sun gudu da shi

Wadansu da ake zargin matsafa ne da ba a gane ko su wane ne ba sun sare hannun hagu na wani magidanci mai suna Muhammadu…

Wadansu da ake zargin matsafa ne da ba a gane ko su wane ne ba sun sare hannun hagu na wani magidanci mai suna Muhammadu Bello a Zariya, Jihar Kaduna sun tafi da hannun.

Da yake bayyana yadda abin ya faru ga wakilin Aminiya, Malam Muhammadu Bello ya ce “A ranar Litinin 14 ga Janairu da misalin karfe 9 na dare ina dawowa daga wajen kasuwancina na sayar da fitilun da ake hadawa, a tsakanin unguwarmu da Jushin Waje, wadda rafi ne ya raba mu, ta bayan barikin sojoji; sai na tarar da wadansu mutane su biyar da bakaken kaya a jikinsu kuma suna dauke da tociloli a kusa da rafi. To amma ba su da wata muguwar kama, domin na dauka ma ma’aikata ne, don haka ban damu ba har ma sallama na yi musu amma ban san ko daya daga cikinsu ba.”

“Ina zuwa sai daya ya ce kai daga ina ka fito? Na fada musu sai suka ce in kashe wutar tocilata, sai na kashe. Suka karbi buhun da ke hannuna wanda na saya wa yarana tsarabar nama da kosai da burodi, sai kawai na ga sun kama ni sun bankare, suka shake wuyana da kebul. Muka kama kokuwa da daya, kafin su tarar mini suka sare hannuna suka jefa ni cikin tabo har sai da na suma. Da Allah Ya sa na farfado sai na kasa fitowa daga cikin ruwa, har sai da gari ya waye mutane suka same ni a cikin tabo. Aka ciro ni, sannan aka gaya wa ’yan sanda, sannan aka kai ni asibiti,” inji shi.

Ya ce, “Sun kwantar da ni a asibiti sai da na kwashe mako uku kafin a sallame ni in dawo gida. Ina komawa duk bayan kwana 3 ana wanke mini hannun. Abin da ya dame ni shi ne ban san abin da za su yi da hannun nawa ba.”

Kan yaya aka yi ya san cewa matsafa ne ko ’ya’yan kungiyar asiri ne suka yi masa haka? Sai ya ce “Abin da ya sa na ce ’yan kungiyar asiri ne saboda sun tafi da hannun nawa da suka sare kuma ban da shi hannun nawa ba su dauki komai ba a cikin kayan nawa kuma an duba koda za a gani, ba a gani ba.”

Wani ma’aikacin asibitin da aka kwantar da shi, mai suna Malam Hamza Abubakar ya ce wani dan sanda ne da wadansu mutane suka kawo musu shi da safe a ranar 15 ga Janairu, cikin mawuyacin hali. “Amma cikin hukuncin Allah muka gyara shi, muka wanke sannan muka fara yi masa magani kuma muka gyara hannun da aka sare, wato muka gyara sauran jijiyoyin da ba su daidaita ba, domin ka san sarewa aka yi da karfin tsiya. Don haka dole a gyara shi kafin a fara sa magani kuma an yi nasara domin mun sallame shi sai dai yana zuwa ana wanke hannun,” inji shi.

Aminiya ta tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan Tudun Wada, DPO Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin. Kuma ya ce lamarin ba yana yankinsa ba ne yana yankin ofishin Kasuwar Mata ne, don haka bayan sun kai shi asibiti sai suka mika wa DPO na Kasuwar Mata.