Da Dumi Dumi

Matsalar matasan Hausawa ita ce raina sana’a – Abdullahi Abubakar

Abdullahi Abubakar
Abdullahi Abubakar

Wani matashi mai suna Abdullahi Abubakar da ya shafe shekara 15 yana sana’ar dinkin kwado da linzami a Unguwar Sabo Ibadan a Jihar Oyo, ya ce bai kamata matasanmu Hausawa su rika raina sana’a ko aiki ba, wanda yin haka ne ke janyo karuwar marasa ayyukan yi a tsakanin matasa a garuruwan Arewa.

Abdullahi Abubakar wanda ya ce ya yi karatun boko zuwa karamar sakandare, ya shaida wa Aminiya cewa, “Matsalar halin yau ta rashin kudi daga bangaren iyayena ne ya sa ban ci gaba da karatu ba, amma maimakon haka sai na koma ga koyon sana’ar dinkin kwado da linzami daga mahaifina, inda na koya a wancan lokaci kuma nake koyarwa a yanzu. A cikin wannan sana’a da na yi gadonta, na yi aure kuma ina taimakon mabukata da wasu bukatun yau da kullum.”

“Abin kunya ne kuma abin bakin ciki a ga matashin Bahaushe zaune babu sana’ar da yake yi balle aiki. Wannan ya biyo bayan raina sana’a da aiki ne da ta dabaibaye matasanmu da suke jiran samun wani babban aiki ko mika musu dimbin kudi a matsayin jari. Muddin ba ka wahala ba wajen tasowarka, to babu yadda za ka iya juya kudin da aka ba ka domin ba ka san darajarsu ba. Haka za ka barnatar da kudin ba tare da cin moriyarsu ba, a karshe ka koma roko da aikata miyagun ayyuka,” inji shi.

Ya ce “Wani abin da ke faranta raina shi ne yadda Yarbawan da muke zaune da su a nan Ibadan za ka ga mafi yawansu sun yi karatun boko har zuwa manyan makarantu suna girmama ayyuka da sana’o’i har zuwa lokacin da lamarin zai daukaka. Amma ba haka lamarin yake ga Bahaushe ba.”

Da yake karin haske a kan irin dinke-dinken gargajiya da yake yi, Abdullahi Abubakar ya ce “Muna hulda da manyan mutane Hausawa da Yarbawa har da sarakuna, wadanda suke kawo mana dinkin gargajiya da suke so a yi musu. Kuma kusan a kowane garin Allah ya waye za ka abokin hulda ya kawo mana aiki. Muna cajin kudin aikin da ya kama daga Naira dubu biyu zuwa sama a kan irin aikin da ake so. Yawa ko karancin kudin aiki ya danganta ne da darajar irin aikin da ake yi,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Abdullahi Abubakar ya ce, “Sana’ar dinkin kwado da linzami tana da muhimmanci musamman wajen daukaka al’adun da muka yi gado kaka da kakanni, kuma akwai manyan mutanen Yarbawa da suke zuwa wurinmu domin bukatar a yi musu irin wannan dinki namu. Ina kira ga matasa ’yan uwana musamman Hausawa su dawo daga rakiyar zaman dirshan, su nemi kananan sana’o’in da za su fara zuwa lokacin da Allah Zai sanya musu albarka Ya yaye musu kuncin rayuwa.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya