Search
Subscribe
Matsalar samar wa Bangaren Shari’a kasafi mai kyau

Matsalar samar wa Bangaren Shari’a kasafi mai kyau

Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a  Ibrahim Tanko Mohammed, a kwanakin baya ya yi karin haske game da matsalar da ta dade tana ci wa sashen shari’ar kasar nan tuwo a kwarya. Ya yi magana ce lokacin bikin Shekarar Shari’a na Kotun Koli tare da gabatar da sababbin manyan lauyoyi (SAN) 38. Babban Jojin ya yi watsi da tunanin da wadansu ke yi cewa Sashen Shari’a ba ya da ’yancin gudanar da harkokinsa cikin walwala; inda ya ce Bangaren Shari’ar na cin gashin kansa da tsarin mulki ya tanadar masa, ba tare da katsalanda daga wani bangare ba. Ya ce: “Ba mu bayar da kai bori ya hau ga muradun wani ta yadda zai juya mu yadda ya ga dama. Idan dai har akwai wanda za a ji tsoronsa, to shi ne Allah Madaukakin Sarki. Ba za mu taba zama ’yan amshin shatan kowa ba duk girman mukaminsa cikin al’umma.” Sai dai Babban Jojin ya amince cewa cin gashin kan Sashen Shari’ar har yanzu yana da tasgaro lura da kudin gudanar da ayyukansa sakamakon yadda kasafin kudin bangaren yake da karanci kuma yake raguwa tamkar kudin guzuri lokaci zuwa lokaci. Don haka, ya yi kira da a kara wa sashen kudi a kasafin kudin shekara-shekara don tabbatar da ya samu cikakken ikon tafiyar da al’amuransa yadda ya dace. Mai shari’ar ya fito da batun baro-baro sa’ilin da ya yi kiran cewa ya kamata a kalli Sashen Shari’ar a zaman mai cikakken ’yancin kansa a zahiri, a duk fadin kasar nan.

Tsokacin Babban Jojin ya kara fito da batun rashin samar wa Sashen Shari’ar wadattun kudin gudanarwa a zaman abin musayar miyau tsakanin ’yan kasa. Rawar da doka da oda ke takawa dai wani muhimmin batu ne wanda bai misaltuwa cikin tabbatar da bin dokoki a zamantakewar al’umma. Don haka, lallai ne a tabbatar da cikakken iko da cin gashin-kai ga Bangaren Shari’ar. Cikin aikin da sashen ke gudanarwa na fassara dokoki, ’yancin fassara doka ba tare da nuna fifiko ga wane bangare ba a duk wata rigima, ya kasance jigo cikin aikace-aikacen sashen na shari’a. Kalaman na Babban Jojin ba za su yi wa ’yan Najeriya da dama dadi ba, idan aka yi la’akari da ire-iren abubuwan da suka faru a ’yan kwanakin nan a kotunan kasar nan. Ba tare da duk wata inda-inda ba, ’yan Najeriya da dama za su tabbatar da alkalai a mafi yawan kotunan kasar suna bayar da kai bori ya hau – a hukunce-hukuncen da suke zartarwa, wadanda babu adalci cikinsu sam. Don haka ake ganin, ikirarin da Babban Jojin ya yi na Sashen Shari’ar na cin gashin kansa, ba zai zama hakikanin halin da sashen ke ciki ba gaba dayansa; sakamakon yadda galibin alkalai ke zama ’yan amshin shatan wadanda suke ba su na goro.

Sai dai a wani abu da ya zama tamkar gaskata magautan sashen shari’ar, shi ne fita fili da Babban Jojin ya yi wajen yaye hijabi game da matsananciyar matsalar samar wa sashen kudin gudanar da aiki. Lura da amincewa da ya yi na karancin kudin sashen, ya nuna yadda Bangaren Shari’ar ke yawo da kokon bara yana neman karin kudin gudanarwa; kuma lamarin ya nuna abin ya kai matuka – da ke bukatar lallai ne a duba tare da daukar matakin gaggawa a kai. Kamar yadda ya bayyana, Bangaren Shari’ar a wasu jihohi na takun- saka da gwamnatocin jihohin wadanda suke tilasta alkalai lallai su juya akalar shari’a yadda masu mulkin suke so. Ba tare da shakku ba, lamari irin wannan da Babban Jojin ya furta, ka iya sanya bara-gurbin alkalai a wadancan jihohi su zamana ’yan maula a wajen da bai dace ba ko da kuwa hakan ka iya shafar hukunce-hukuncen da za su zartar.

Sai dai har yanzu akwai abin karfafa gwiwa kasancewar yadda Babban Jojin ya yi gargadin cewa Bangaren Shari’ar ba zai taba mika wuya wajen neman gashin kan kudin gudanarwarsa ba ko ta halin kaka, inda ya ce kamata ya yi a kyale Sashen Shari’ar ya “tunkari matsalolinsa da kansa.” Wannan matsayin ya yi daidai da tanadin dokar kasa da abin da jama’a suke sa ran gani daga Sashen Shari’ar. Wani abin lura, shi ne yadda mahukunta da dama tare da rufa bayan masu jibi ke kara kira da babbar murya a samar wa Bangaren Shari’ar cikakken ikon kudin gudanar da harkokinsa yadda ya kamata. Yanzu nauyi ya rataya kan wuyan Majalisar Dokoki ta Kasa wadda ke da iko bisa tsarin mulki wajen raba kudin kasafi, da yin gyaran fuska ga wannan mummunan yanayin da Bangaren Shari’ar ya samu kansa  a ciki.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin