✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar talauci da rashin aikin yi a Najeriya: Laifin gwamnati ko na al’umma?4

Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a…

Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Hukuma za a dora wa laifi – Sani Azare

Alhaji Sani Azare: “Matsalar talauci a kasar nan, laifin hukuma ne saboda ta gaza wajen samar da ayyukan yi ga jama’arta, sai dai wasu al’umma kalilan da ke da madafun iko ko kuma wadanda suka mara wa baya a harkokin kasuwanci ko na kwangila. Aiwatar da ayyukan da za su habaka tattalin arzikin kasa kamar taimaka wa manoma da makiyaya da masu masana’antu, ba ta ba su muhimmanci ba. Hakan ya jawo tashe-tashen hankula, wanda talauci da rashin aikin yi ga jama’a ya haifar.”