Da Dumi Dumi

Matsalar tsaro: Ba canja shugabannin tsaro ne mafita ba – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce ba canja shugabannin tsaro na kasar nan ne mafita ba, kan matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan.

Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen wa’azin kasa da kungiyar ta gudanar a garin Jos, a ranar Asabar da Lahadin da ta gabata.

Ya ce maganar tsaro ta kowa da kowa ce, a Najeriya. “Don haka idan muka yi niyyar mu taru mu gyara harkokin tsaro a Najeriya, za mu a iya gyarawa.”

Sheikh Jingir ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da masu hanu da shuni, su bude kamfanoni da masana’antu a kasar nan, domin a samar wa al’umma ayyukan yi.

Ya ce idan aka samar wa jama’a ayyukan yi, za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

ADVERTISEMENT

A jawabin Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa na Majalisar Wakilai kuma dan Majalisa mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/ Kanam da ke Jihar Filato, Alhaji Yusuf Adamu Gagdi ya bayyana cewa babu shakka akwai gyara kan yadda shugabannin tsaron kasar nan suke tafiyar da tsaron Najeriya.

Ya ce amma duk da haka, ya kamata a yaba musu, domin abubuwan da suka shafi tsaro a kasar nan, su ma sun rasa rayukansu.

Ya ce ya kamata a duba a gani me gwamnati take yi, wanda ba ya biyan bukatar jami’an tsaron kasar nan. Idan gwamnati ta yi wannan za a samu canji kan matsalar tsaro da ake fama da ita.

Ya ce a makon jiya ya gabatar da wani kudiri a majalisa inda yake son a yi gyara wajen ganin an sanya jama’a cikin harkokin tsaro a kasar nan. Ya ce yin haka zai kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali .

Alhaji Yusuf Gagdi ya yi bayanin cewa yanayin tsaron Najeriya, kafin Shugaban Kasa Buhari ya zama Shugaban Kasa, ya bambanta da yadda yake yanzu, domin an samu gyara mai yawa.

“Yanzu bama-bamai da ake sanyawa a baya babu. Amma wasu abubuwa suna son su dawo, don haka muke kira ga Shugaban Kasa a sake duba tsarin tsaron kasar nan, domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali,” inji shi.

Shi ma a nasa jawabin Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya mika godiyarsa ga kungiyar, kan yadda ta dauki dawainiyar bakin da suka halarci wajen wannan wa’azi.

Ya ce wannan taron wa’azi alama ce ta tabbatuwar zaman lafiya a Jihar Filato wanda shi ne babban aikin da ya sanya a gaba.

‘’Sai da zaman lafiya ne za a samu cigaba a fannonin rayuwa. Don haka aikin da za a samu zaman lafiya, aiki ne da ya rataya kan kowa da kowa.  Don haka gwamnati take tunanin ta samar da tsaro, tun daga matakin kowace al’umma. Ta hanyar samar da jami’an tsaro a cikin al’umma, wadanda za su rika kula da harkokin tsaro a cikin al’umma’’.

Gwamnan wanda Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Malam Muhammad Muhammad ya wakilta, ya yabawa kungiyar kan irin wa’azin zaman lafiya da take gudanarwa a Najeriya da kasashen waje.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya