✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Gbajabiamila ya nemi China ta tallafa wa Najeriya

Shugaban Mjalisar Wakilai ta Kasa Femi Gbajabiamila ya bukaci taimakon gwamnatin kasar China wajen kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kasar nan. Shugaban ya…

Shugaban Mjalisar Wakilai ta Kasa Femi Gbajabiamila ya bukaci taimakon gwamnatin kasar China wajen kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Shugaban ya ce Najeriya da China suna dasawa a bangarorin tattalin arziki da siyasa don haka ne ya kamata a samu hadin kai a tsakanin kasashen biyu ta bangaren soja don kawo karshen matsalar tsaro da Najeriya take fuskanta.

Shugaban yana magana ne a yayin da ya karbi bakuncin Jakadan China a Najeriya Mista Zhou Pingjian, wanda ya kai masa ziyara a ofishinsa a  Abuja a ranar Talata. Gbajabiamila ya kara da cewa a wannan lokaci na jarrabawa Najeriya tana neman taimako daga ko’ina.

“Ina neman taimakonku ne ta fannin alaka. Babbar matsalarmu a yanzu ita ce ta tsaro kuma muna maraba da taimako daga ko’ina.

“Don haka, ta bangaren soja za mu yi farin ciki idan muka samu taimakonku a  yanzu,” inji Gbajabiamila.

Da juya kan maganar cutar Kurona kuma, Gbajabiamila ya jinjina wa Gwamnatin China kan namijin kokarin da ta yi don ganin wannan cuta ba ta yadu zuwa wasu kasashe ba.

Ya ce Najeriya za ta taimaka wa kasar China don kawo karshen wannan annoba, inda ya ce akwai bukatar ci gaba da wayar da kan al’umma don ganin ba su samu fargaba ba game da cutar.

Haka kuma Shugaban ya tabbabatar wa kasar China cewa za ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan kawayen Najeriya ta bangaren harkokin tattalin arziki da siyasa.

“Kun kasance jigo a harkokin kasuwancinmu. Kamar yadda ka fada, Dala biliyan 19 ba kananan kudi ba ne, don haka muna duba hanyoyin inganta dangantakarmu da ku ta fannin kasuwanci da  siyasa.

“Kuna fuskantar kalubalen cutar Kurona, amma mun yaba kokarinku zuwa yanzu. Kun gina asibiti mai gadaje 1000 a cikin mako daya ga wani kuma mai dauke da gadaje 1600.

Jakadan Mista Pingjian ya fada wa Shugaban cewa kasarsa tana daukar Najeriya a matsayin babbar kawa musamman ta fannin tattalin arziki inda ya ce a yanzu huldar kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu ta kai ta zunzurutun kudi har Dala biliyan 19.

Ya bukaci a ci gaba da zaman lumana a tsakani kasashen biyu, inda ya ce kasar China za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya don ganin ta cimma bukatunta.

Da ya juya kan batun cutar Kurona, Jakadan ya ce kasarsa tana yin dukkan abin da ya kamata don ganin ta shawo kan wannan annoba.

Ya ce zuwa yanzu babu wani dan Najeriya mazaunin kasar China da ya kamu da cutar, don haka kasar za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata wajen ta kare muradun ’yan Najeriya.

Ya ce “Za mu tsare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya da suke zaune a kasar China.”  inda ya ce kasarsa tana da tabbacin ganin bayan wannan annoba.