Da Dumi Dumi

Matsalar tsaro: Za a samar da rundunar hadaka a Kudu maso Yamma

Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma lokacin taronsu na nemo mafita kan matsalolin tsaro a yankinsu
Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma lokacin taronsu na nemo mafita kan matsalolin tsaro a yankinsu

Gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma da suka hada da Legas, Ogun, Oyo, Ondo, Osun da Ekiti sun samu izinin kafa rundunar tsaro ta hadaka daga ofishin Babban Mai bada Shawara kan Tsaron Kasa (NSA) a domin inganta harkokin tsaro a yankunansu.

Tun farko gwamnonin jihohin sun yi taron ci gaban yankunan nasu inda suka yi zama sau biyu a garin Ibadan da ke Jihar Oyo a watan Yunin bana, sannan suka yi wani zama a garin Akure babban birnin Jihar Ondo inda suka tattauna al’amuran da suka shafi tsaro da ci gaban yankin.

A karshen taronsu na garin Ibadan Shugaban Gwamnonin Kudu maso Yamma, kuma Gwamnan Jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu ya shaida wa manema labarai cewa, yanayin tsaron yankin zai sauya daga watan Agustan nan. Ya ce shirin da suke na kaddammar da shirin kowane Gwamna a yankin ya samu motocin sintiri da za a yi amfani da su a jiharsa.

Bayanai sun ce rundunar tsaron hadakar da gwamnonin za su yi amfani da ita ta kunshi ’ya’yan kungiyar OPC da kungiyoyin maharba da mafarauta da kuma wadansu da za su yi aiki wajen tattaro bayannan asiri. Ma’aikatan rundunar za su yi aikin sintirin a manyan hanyoyi da sassan dazukan yankin, kuma za su yi aiki da sarakunan gargajiyar yankin.

ADVERTISEMENT
Share