✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsayin Abba Kyari a Najeriya

Tun bayan nada shi shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a watan Agustan 2015, sannu a hankali Abba Kyari…

Tun bayan nada shi shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a watan Agustan 2015, sannu a hankali Abba Kyari ya zamo wani mai fada a ji a harkar mulkin Najeriya.

Kusancinsa da shugaban kasa da kuma yardar da Buhari ya yi da shi sun sa ya zama kashin bayan gwamnati, musamman ma kasancewar shugaban kasar ya sakar masa ragama, lamarin da ya kai ga Uwargidan Shugaban Kasar Aisha Buhari da wasu a Fadar Shugaban Kasar da zargin cewa ya saka shugaban kasar a keji ya rufe.

Shekaru na tafiya, ikons ana karuwa, har aka sake nada shi a karo na biyu a matsayin shugabn ma’aikatan fadar shugaban kasa bayan an sake zabar Buhari a karo na biyu a 2019.

Lokacin da yake kaddamar da majalisar ministocinsa a watan Agusta bara, shugaban kasar ya umarci ministocin da su mika duk wani rahoto gare shi ta hannun Abba Kyari, lamarin da ya sa wasu ’yan Najeriya da ke ganin tamkar ya mika ragamar Mulki a hannun shugaban ma’aikatan ne suka fusata.

Ko a watan Fabrairun da ya gabata wata takarda da aka kwarmato daga Ofishin Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Sha’anin Tsaro, Babagana Mungono, ta zargi Shugaban Ma’aikatan da wuce gona da iri ta hanyar saba umarnin shugaban kasa, da gudanar da taruka da manyan hafsoshin tsaron kasa, da kuma yin katsalandan a harkar tsaron kasa, ciki har da bayar da kwangilar sayo makamai.

Tun kafin waccan kurar ta lafa, Malam Abba Kyari ya tafi Jamus, inda ake zargin ya kamu da cutar coronavirus, don sa hannu a kan wata yarjejeniya ta samar da makamashi a madadin gwamnatin Najeriya.

Bayan dawowarsa ranar 13 ga watan Maris 2020 Abba Kyari ya koma bakin aikinsa, inda aka rawaito ya gana da wasu gwamnoni da wasu jami’an gwamnatin kwanaki tara kafin a tabbatar da gwajin ya kamu da cutar coronavirus.

A ranar 21 ga watan Maris, Abba Kyari ya aike da wata takarda da ke jan kunnen ’yan majalisar tarayya da suka dawo daga kasashen waje cewa su mika kansu don a yi masu gwajin cutar COVID-19 saboda rahotanni sun ce sun ki yin hakan.

Kwana biyu bayan nan aka tabbatar da shi ma kansa yana dauke da cutar.

Wasu daga cikin iyalansa da suka zanta da ’yan jarida sun ce bai killace kansa ba ne saboda a lokacin Jamus ba ta cikin kasashen da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce suna da hadari.

Labarin cewa ya kamuy a sa manyan mutane da dama sun firgita, musamman wadanda suka gana da Shugaban Ma’aikatan na fadra Shugaban Kasa.

Haka nan kuma labarin ya haddasa damuwa game da lafiyar Shugaba Buhari ganin kusancin da ke tsakaninsu.

Ko da yake sakamakon gwajin da aka yi wa Shugaba Buhari ya nuna bai kamu da cutar ba, hankali ya tashi game da lafiyar Abba Kyari, saboda sanin cewa da ma yana fama da wata larura.

Bayan kwana biyu ba ;abari sai aka ji an dauke shi zuwa Legas don a kula da lafiyarsa, a maimakon cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Abuja.

Dag abaya ta bayyana cewa Abba Kyari ya yi shiri na kashin kansa ne na duba lafiyarsa kamar yadda ya fada a wata wasika da ya rubuta daga inda yake killace.

Malam Abba Kyari dai ya yi digirinsa na farko ne a Ilimin Zamantakewa a Jami’ar Warwick, wadda ya gama a 1980, sannan ya yi wani digirin a Shari’a a Jami’ar Cambridge, dukkansu a Ingila, ya kuma zama lauya a Najeriya a 1983.

Shekara guda bayan nan ya yi digiri na biyu a Shari’a a Jami’ar Cambridge, sannan daga bisani ya halarci Cibiyar Nazarin Al’amuran Gudanarwa da ke Swtitzerland.

Bayan dawowarsa Najeriya ya yi aiki a kamfanin lauyoyi na Fani-Kayode & Sowemimo na dan wani lokaci.

Daga 1988 zuwa ya rike mukamin Edita a kamfanin New Africa Holdings Limited da ke Kaduna sannan ya yi kwamishina a jiharsa ta Borno a 1990.

Ya yi aikin banki a lokutan daban-daban, har ya kai matsayin daraktan mulki a bankin UBA kafin daga bisani ya zama babban daraktan bankin.

A shekarar 2002 aka nada shi darakta a hukumar gudanarwa ta kamfanin Unilever, daga baya kuma aka saka shi a hukumar gudanarwa ta kamfanin Exxon Mobil.

Abba Kyari mutum ne mai shiru-shiru, amma ya haddasa tirka-tirka a lokuta daban-daban a Gwamnatin Buhari, kuma duk y aga bayansu.