Search
Subscribe
Matsayin mata a siyasar Najeriya

Matsayin mata a siyasar Najeriya

Mata sun sami dama a siyasar Najeriya, inda suka fara da rike manyan mukamai a shekarun da suka wuce. Wannan ke nuna cewa mata sun taso har a ba su matsayin da ya dace a al’ummance, domin babu mukamin da namiji ya rike a siyasance da mace ba ta samu dama ko da takarar wannan matsayin a kasar nan.
Mace a matsayinta na mutum, ta kasance uwa, ’ya, kanwa, mata ko diya za ta zama a karkashin maza, yayin da za su yi aiki tare, duk da cewa takan kasance mahaifiya, wadda ke da hakkin dora maza a kan hanyar zama mutanen kirki, a kan haka idan al’umma ta bace har da laifin mata domin ba su ba ’ya’yansu tarbiyya ba.
Sai dai kash, mata na samun nasara, yayin da ’yan uwansu mata da maza ke fuskantar barazana daga gare su, musamman domin an fi sa rai za a samu sauki idan mace ta dare sama. Mace a matsayin uwa, kulawarta ba ta tsaya a kan mata ba! Amma a yau me ta yi wa ’ya’yan kishiya balle ku ’ya’yan makwabta?
Babbar barazana da ci gaban mata ke haifarwa shi ne, mata na barin dabi’ar da Ubangiji ya yi masu na haihuwa da kula da ’ya’ya! Sukan gwammace su yi sana’a, su cika burinsu kuma wannan tunanin na samun karbuwa a wajen ’yan mata matasa, wasu ko haihuwar ma ba ta gabansu, su
dai su samu daukaka a duniyance!
Sannan mata ne makiyan kansu, su suke hana ’yan uwansu mata ci gaba ko shawarar yadda za su yi gaba sun gaza dora raunana a cikinsu. Yayin da mace daya ta samu dama sai ta ture sauran ’yan uwanta gefe, ta ci gaba da cin karenta ba babbaka, ta hanyar yin kwalliya da tinkaho. Hakan idan muka kalli kungiyoyi da sana’o’i kamar rubutu za mu ga matan da suka samu daukaka a harkar ba su kokarin kawo ci gaba ga ’yan uwansu, su dai sun zama kalluba cikin rawuna, su bar sauran a matsayin masu karanta littattafan da suka rubuta! Nan gaba kadan zan yi bayanin yadda mata marubuta za su ilimatar da mata makaranta.
Wata fitina ga ci gaban da mata suka samu ita ce ta son jayayya da maza, duk da cewa Ubangiji ya fifita mazaje a kan mata ta fuskoki da dama, idan muka kalli yadda aka hallici namiji jikinsa ba daya yake da na mata ba, amma sai ka iske har atisaye, irin kwallon kafa mata sun shigo don su buga, duk da cewa hakan bai dace da dabi’arsu ba.
Musamman idan muka kalli yadda aka hallici namiji jikinsa ba laushi, wasu wuraren kamar katako yake, sai ka ce bakanike, sabanin mace wadda jikinta kamar katifa yake, shi ya sa duk wasu wahalhalu sun fi dacewa da mazaje. Wannan kuma ya mayar da mace a matsayin ’yan gata, masu bukatar kulawa da tsaro daga wajen mazajen.
Akwai dalilai da dama da suke sa mutane, musamman maza da wasu mata ba su zaben mata idan suka fito takara. Da farko, yaushe matar ke shigowo cikin jama’a idan ita ’yar mutunci ce? Domin al’adu da addinai sun nuna cewa mutuncinta shi ne a gidansu, gaban iyaye, idan ta isa aure kuma za a same ta a dakin mijinta! Sannan an gwada an ga ba su tsallake hadarin cin hanci da rashawa ba, musamman domin sukan yi amfani da son ransu a kusan duk lamarin da suka samu kansu.
Wasu matan sun gane ba abin da ya fi muhimmanci a rayuwa sai su kiyaye dabi’ar da aka hallice su, ta hanyar yin barci da wuri da tashi a kan lokaci, ba ruwansu da wani buri. Haka iyayensu ba su goyon bayan biyewa karatun zamani, sun gwammace ’ya’yansu su samu mazajen da za su kula da dawainiyarsu ba tare da cewa su matan za su rika kawo wata gudunmuwa ba.
Hasali ma, ba su tunanin wai idan mijin ya saki diyarsu, domin su a ganinsu ko hakan ta faru za su samu wani angon, watakilla wanda ya fi mijin farkon alheri da albarka.
Daga karshe dole a ba kowa matsayinsa, domin sau da yawa idan aka ba mace wani mukami akan tashi da takaici, musamman idan abin da ya shafi shugabanci ne, koda gida ne ta zama shugaba sai an samu sabani. Akan samu kalilan da suke kwatantawa, kuma ina fata za a samu wasu mata ministoci, kwamishinoni ko ciyamomi, kai koda matan gwamnoni ne a jihohi, da za su yi irin wannan hobasan na kawo ci gaba ta yadda za a tafi tare.
Daure ya rubuto daga kofar kaura, Katsina (+2347035986444)

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin