✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulidi: Gwamnati ta ba da hutu ranar Alhamis

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2020 a matsayin ranar hutu domin bikin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W). Ranar ita ce…

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2020 a matsayin ranar hutu domin bikin ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Ranar ita ce ta zo daidai da 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wata na uku a kalandar Musulunci kuma ranar da ta dace da ta haihuwar Ma’aikin.

Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya sanar da ba da huutun a madadin gwamnati ta bakin kakakin ma’aikatarsa, Mohammed Manga a ranar Talata.

Sanarwar ta taya daukacin al’ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar tare da yin kira gare su da su yi koyi da halayen  Ma’aikin, musamman na kaunar juna, hakuri da kuma son zaman lafiya.

Aregbesola ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya musamman Musulmai da su kaurace wa rikici, karya doka da tayar da zaune tsaye, yana mai cewa a matsayin Najeriya na kusa a nahiyar Afirka, ya kamata ta zama abar koyi ga takwarorinta.

Ya kuma gargade su da su guji yin duk wani abin da zai raba kan al’umma, su kuma taimaka wa manufar Shugaba Buhari ta ganin an gina kasa abar alfahari ga kowa.

Musulmai a fadin duniya kan yi shagulgulan ranar Maulidi, kasancewar ita ce aka haifi annabi Muhammad (S.A.W) sama da shekaru 1400 da suka shude a birnin Makkah na kasar Saudiyya.