✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulidi na nuna karfin Musulunci ne –  Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya. Jagora a Darikar Tijjaniyya ya tattauna da…

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya. Jagora a Darikar Tijjaniyya ya tattauna da Aminiya a Bauchi kan muhimmancin mauludi don murnar kewayowar ranar da aka haifi Annabi Muhammadu (SAW), inda ya ce maulidin na nuna karfin Musulunci:

 

Watan Rabi’ul Auwal ya zagayo, me Shehi zai ce dangane da falalar da ke cikin wannan wata kuma me ya kamata Musulmi su yi?

Alhamdu lillahi, muna godiya ga Allah da Ya ba mu babbar ni’ima, don duk duniya babu ni’imar da ta kai samun Manzon Allah Annabi Muhammadu (Sallalahu Alaihi Wasallama), saboda haka da farko ina taya al’ummar duniya murnar shigowar watan maulidi, watan murna, watan shigowar alheri, watan da aka haifi fiyayyen halitta. Kowa na murna da wannan wata da Annabinmu ya zo a cikinsa. Alhamdu lillahi, sai mu kara gode wa Allah da Ya yi mu ’yan Adam, Ya yi mu Musulmi kuma Ya sanya mu cikin fiyayyun al’umma. Mu ne al’ummar Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Shi kuma wannan wata, yadda Allah Ya sa muka ga farkonsa, Allah Ya sa mu ga karshensa lafiya. Allah Ya sa mu samu dacewa da alheri masu yawa da ke cikinsa. Yadda watan ya saba zuwa mana da alherai, ya kwaso mana ya kawo mana, muna fata Allah zai kara mana wannan ni’ima, kuma muna rokon Allah Ya sa albarkacin wannan wata Ya kawar mana da sharri da bala’o’i. Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. A kullum irin wannan lokaci da kowane lokaci, masoya Annabi da ke damuwa da shi, su suke yin  Maulidi. Saboda haka ne kowane Musulmi ke murna da wannan wata saboda a cikinsa ne aka haifi mafi daraja, wanda ya kawo mana abu mafi daraja da girma. Kuma darajar abin da ya kawo maulidi shi ne haihuwar Annabi da aka yi a cikin watan, Musulmi su yi ta murna su yi ta gode wa Allah, su yi ta zikirori da karatun Alkur’ani don nuna farin ciki da gode wa ni’imar da Allah Ya yi mana, na samun Annabi (SAW).

Sheikh, mene ne ma’anar maulidi?

Maulidi na da ma’ana biyu a Larabce, wato wurin da aka haifi mutum da kuma watan da aka haife shi. Hakan ne ya sa aka ce a yi Hajji da Umarah wato maulidin garin da aka haifi fiyayyen hallita ke nan. Sannan maulidi na wata kuma shi ne wanda ake yi yanzu cikin wannan wata na Rabi’ul Auwal. A dunkule dai Maulidi nuna godiya ne ga Allah da kuma bayyana murnarmu a fili da kuma boye. Allah Yana cewa “Ku gode wa ni’imar Allah in da gaske kuke yi ku masu kadaita Allah ne, masu bauta maSa.” Kullum Ya yi muku alheri to ku gode maSa. Babu wata ni’imar da ta zo duniyar nan da ta kai zuwan Annabi Muhammad (SAW) “Wa ma arsalnaka illa rahmatan lil’alamin.” A bisa haka muke nuna godiyarmu, mu gode wa Allah a duk lokacin da watan ya zagayo.

Manzon Allah ya shigo mana duniya, ya zo ya yi shekara 63 wato shekara 21 sau uku ko kuma shekara 7 sau tara. Godiyarmu ba ta tsaya nan ba, muna kuma gode wa Allah da Ya sanya mu daga cikin wadanda suka yi imani da abin da ya zo mana da shi kuma muke bin tafarkinsa har muke raya watan da aka haife shi da murna da kuma nuna soyayyarmu a fili da boye. Wannan abin godiya ne ga Allah.

Al’ummar Musulmi da kungiyoyi na yin zagayen gari ranar maulidi, mene ne muhimmancin yin haka?

Hakan na nuna karfin Musulunci da taron al’ummar Musulmi da girmama abin da Allah Ya girmama. Dama ai irin wannan maulidin da kuma zagayen garin, ana yin su ne don nuna murna, a nuna murna a fili amma in aka zauna ba a yi wani abu ba, ka ga ai ba a nuna murnar ba ke nan. Shi ya sa muke nuna murna a ko’ina, lungu da sako a yi wa Allah zikiri, a kuma yi wa Annabi salati, a karanta Alkur’ani, a bayyana wa duniya tarihinsa don al’umma su san kyawawan dabi’unsa, su yi koyi da su. A lokacin da ake zaga garin nan, ana murna da ranar haihuwar Annabi, mutumin da ba Musulmi ba, idan ya zo ya tarar da babu wajen wucewa idan ya ce ‘What happen, Mene ne haka, me ya faru haka ne?’ Sai a ce masa ai ‘Birthday Celebration’ ne ake yi na Prophet Muhammad (SAW). Zai girgiza kansa ya ce haka! Ka ga shi an sanya masa wani karatu a kwakwalwa, zai kama tunanin cewa ashe haka Annabin nan yake a duniya? Daga nan zai tsunduma neman tarihin wannan Annabin daga nan kuwa in Allah Ya sa mai rabo ne sai ka ga ya ribanci wani abu na daga falalar Annabi, tunda Manzon Allah rahama ne ga kowa da kowa, Rahamatul lil-alamina.

Shi maulidin nan ma yanzu har cikin hutun gwamnati aka shigar da shi saboda muhimmancinsa. A da can baya ba a sanya shi ba, har hakan ya sanya wadansu ke mamaki, wai me ye sa ake dakatar da aiki ga baki daya a ranar Maulidin Manzon Allah ne? To, abin da ya faru ga wanda bai sani ba, bari in fada masa. A cikin wani lokaci Firayi Ministan Najeriya Sa Abubakar Tafawa Balewa ya hadu da Shehu Ibrahim Nyass, sai Shehu ya ce masa ku biyu ne Allah Ya ba ku Najeriya, kai da Azikiwe. Yana zuwa coci ranar Lahadi, ina ce kai ma kana zuwa Juma’a? Ya ce yana zuwa. Ya ce Azikiwe yana ba da hutu ranar haihuwar Annabi Isa (AS), in ce kai ma kana badawa lokacin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW)? Sai ya ce, na yi maka alkawari daga wannan shekara zan shigar da maulidi cikin hutun da ake yi a Najeriya. Ka ji ta yadda hutun maulidi ya shiga tarihin Najeriya ta hanyar Shehu Ibrahim, saboda muhimmancinsa.

Wacce shawara Shehi zai ba matasa?

Ina shawartarsu da su ji tsoron Allah, su nemi ilimi, su girmama na gaba da su kuma su ji tausayin na kasa da su. Ina shawartar dukkan matasa, cikinsu har da ’ya’yana da almajiraina da dukkan al’ummar Musulmi, kowa ya san wanda yake gaba da shi, ya girmama shi kuma kowa ya san wanda ya girma, ya ji tausayinsa. Ba kamar irin abin da yake faruwa yanzu ba, yadda za ka ga matasa da suke kiran kansu da sunan malamai amma suna zagin wadanda suka grime su, suka fi su ilimi da tsoron Allah cikin Musulunci. Kuma kamar kullum, rokonmu ’yan Najeriya su zauna lafiya da juna. Addu’armu Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. Kuma muna rokon al’ummar Musulmi mu yi ta addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya, Allah Ya kawo karshen wadannan tashe-tashen hankali da kashe-kashe a Najeriya da satar mutane a yi garkuwa da su don neman kudi. Masu neman mu da sharri, Allah Ya mayar musu da sharrinsu kansu. Allah Ya saukar da alheri da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.