Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mawakan APC sun zargi Rarara da rashawa

Mawakan jam’iyyar APC a karkashin Kungiya mai suna All Progressives Congress (APC) Northern Musicians Forum (ANMFO) sun zargi fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara da wadansu mutum bakwai da yin almubazzaranci da kuma rashawa.

Mawakan wanda suka rubuta wasikar ga wadanda ake tuhumar bayan sun kafa kwamiti na mutum 11 a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban riko na kasa na ANMFO, Murtala Mamsa da kuma shugaban kungiyar reshen Babban Birnin Tarayya Abuja, Ahmed Turaki Kaka a matsayin sakatare sun bukaci Rarara da sauran wadanda ake tuhumar da su bayyana gaban kwamitin don kare kansu.

ADVERTISEMENT

An kafa wannan kwamitin bincike na mutum 11 ne bayan zaman da shugabanni kungiyar na jihohin arewacin Najeriya 19 suka yi a garin Jos a makon jiya.

ADVERTISEMENT

Kwamitin ya ce kungiyar ta samu gudunmuwar makudan kadade a hannun wadansu mutane ‘yan jam’iyyar APC, amma an nemi kudaden an rasa.

Kwamitin ya bayyana cewa bayyanar su Rarara ya zama tilas don a gano inda kudaden suka shiga.