✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawaki Fatai Rolling Dollar ya rasu

Fitaccen mawaki Fatai, wanda ake yi wa lakabi da ‘Rolling Dollar’ ya rasu ranar Litinin yana dan shekara 85, a asibitin Ahmadiyya da ke unguwar…

Fitaccen mawaki Fatai, wanda ake yi wa lakabi da ‘Rolling Dollar’ ya rasu ranar Litinin yana dan shekara 85, a asibitin Ahmadiyya da ke unguwar Abule Egba, Legas, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wani na kusa da shi mai suna Kunle Tejuosha ya tabbatar da mutuwarsa, kuma ya ce marigayin bai dade da dawowa daga Amurka ba, inda ya je yin wasa makonni uku da suka wuce.
Tejuosho ya bayyana shi a matsayin babban mawaki wanda ya mutu yana yi wa kida da waka hidima. “Gaskiya Baba, babban mawaki ne, wanda ya sarayar da rayuwarsa yana kida da waka. Yana farin ciki kodayaushe idan yana yin wasa. Mutumin kirki ne, wanda yake jin dadin rayuwarsa kuma ya yi amfani da damar da ya samu. Saboda haka za mu yi kewar rashin sa”. Inji shi
Fatai ya yi fice wajen waka tare da sarrafa garayar zamani. Irin yadda yake da kuzari da kazar-kazar, ya kara janyo masa farin jini a tsakanin matasan da a kowane lokaci suke burin samun lafiya da tsawon shekaru irin nasa.
An haife shi a ranar 22 ga watan  Yulin shekarar 1926 a kauyen Ede da ke Jihar Osun. Ya mutu ya bar matan aure da ’ya’ya masu yawa.
Tuni aka yi jana’izarsa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.