✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawakin Shugaba Buhari, Malam Yala ya ajiye mukaminsa

Fitaccen dan siyasa, kuma mawakin siyasar nan da ya rera wakar ‘Yau Najeriya riko sai mai gaskiya,’ Malam Ibrahim Sale, wanda aka fi sani da…

Fitaccen dan siyasa, kuma mawakin siyasar nan da ya rera wakar ‘Yau Najeriya riko sai mai gaskiya,’ Malam Ibrahim Sale, wanda aka fi sani da Malam Yala ya ajiye mukaminsa.

Yala, wanda shi ne Mai ba Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Honourable Yusuf Ibrahim Zailani, shawara kan harkokin watsa labarai, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram a ranar Talata.

“A jiya 28 ga watan Satumba na 2020 na sauka daga kan mukamina na mai bai wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna shawara kan harkokin watsa labarai.

“Ina mai amfani da wannan damar domin godiya ga Shugaban Majalisar saboda damar da ya ba ni na yin aiki a karkashinsa,” inji Yala.

Malam Yala dan siyasa ne a Kaduna, inda ya kasance Darakta Janar na Yakin Neman Zaben Sanata Uba Sani a zaben 2019.

 

View this post on Instagram

 

I resigned my appointment as S.A media to the speaker KDSHA Hon Yusuf Ibrahim zailani yesterday 28/9/2020. I want to use this platform to thank Mr speaker for the opportunity given to me to serve under him.

A post shared by Ibrahim yala (@real_ibrahim_yala) on