✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maza gumbar dutse: Tunawa da marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha

Allahu Akbar! Masu iya magana na cewa shekara kwana, a ranar Larabar makon jiya ce marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya cika shekara 18…

Allahu Akbar! Masu iya magana na cewa shekara kwana, a ranar Larabar makon jiya ce marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya cika shekara 18 da rasuwa.
Marigayin wanda shi ne Shugaban kasa na 10 a tarihin Najeriya, ya kokarta wajen farfado da tattalin arzikin kasa, ta yadda muna iya cewa ya fi dukkan shugabannin kasar nan taka rawa a wannan fanni, domin a lokacinsa ne asusun waje na kasar nan ya karu daga Dala miliyan 494 zuwa Dala biliyan tara da miliyan 600 a shekara hudu kacal.
Sannan shi ne wanda ya biya kaso mafi tsoka na bashin da ake bin Najeriya, tare da sauya shawarar gwamnatin da ya gada ta sayar da kadarorin gwamnati ga ’yan kasuwa. A cewarsa ba a gina gwamnati domin cin riba ba, sai dai an gina ta ce domin ’yan kasa su more wa alfanunta.
 Kuma ya rage hauhawar farashin kayan masarufi da kashi 54 cikin 100 domin talakawa su ji dadin rayuwa. Abin mamakin kuma shi ne, ya aiwatar da wadannan abubuwa ne a lokacin da farashin gangar danyen mai yake Dala 15 kacal a kasuwar duniya.
 An haifi marigayi Janar Sani Abacha, a ranar 20 ga Satumban 1943, iyayensa Kanuri ne, amma a Kano aka haife shi, kuma a garin Kano ya girma. Don haka ake daukarsa a matsayin Shugaban kasa dan Jihar Kano na biyu a tarihin Najeriya bayan marigayi Janar Murtala Mohammed.
Ga kadan daga abubuwan tunawa game da rayuwa da shugabancin marigayi Janar Sani Abacha:
 1. Marigayi Janar Sani Abacha ya fara aikin soja ne tun daga kurtu, sannan aka yi masa karin girma zuwa mukamin karamin Laftana bayan ya yi wani kwas a kasar Ingila a 1963.
 2. Janar Abacha mutum ne gwanin iya samar da sauyi ta hanyar tsara juyin mulki. Shi ne ya shirya juyin mulkin da ya kawar da gwamnatin da ta hallaka su Sardauna. Shi ne ya shirya juyin mulkin da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki a zamanin soja, kuma shi ne bayan gwamnatin ta sauya akala ya sake shirya juyin mulkin da ya kawar da Shugaba Buhari daga kan mulkin kasar nan.
 3. Janar Abacha ya auri matarsa Hajiya Maryam Sani Abacha a 1965 wadda ta fito ne daga kabilar Shuwa-Arab da ke Jihar Borno. Ita ce kuma ta gina katafaren Asibitin kasa (National Hospital) a Abuja a lokacin da mijinta ke mulki a karkashin shirinta na matar Shugaban kasa. Manufar ginin asibitin ita ce don duba lafiyar kananan yara da mata cikin rahusa, wanda hakan ya sa aka sanya wa asibitin suna National Hospital for Women and Children a wancan lokaci.
  4. Janar Abacha ne Shugaban kasar da bai taba tsallake wani mukami a tsarin mukaman soja ba har lokacin da ya zama Shugaban kasa da mukamin Laftana Janar.
  5.  Shugaba Abacha ba ya da yawan surutu a gaban jama’a. Don haka wasu ke kiransa da ‘dan kurma.’ Duk cece-ku-cen mutane a game da shi, kalmomi kadan yake tofawa, amma kuma duk abin da ya ce zai yi babu kokwanto sai ya aiwatar da shi.
 6. Shugaba Abacha gwani ne a fannin tattalin arziki, domin ya saisaita tattalin arzikin Najeriya a lokacin mulkinsa inda ake sayar da Dala daya a kan Naira 22 a farashin gwamnati, Naira 80 kuma a farashin kasuwar bayan-fage.
 7. Janar Sani Abacha babban aminin marigayi Shugaban kasar Libya Kanar Muammar Gaddafi ne. Kuma yana da matukar kishin Afirka da bakar fata.  Ya taimaka kwarrai wajen samar da hadin kai ga kasashen Afirka a karkashin kungiyar kasashen Afirka (OAU) tare da wanzar da zaman lafiya a kasashen Laberiya da Saliyo.
 8.  Janar Sani Abacha mutum ne da ba ya jure wa raini, shi tamkar sarakunan Larabawa yake. A wurinsa, ka fadi duk abin da za ka fada a kansa ko gwamnatinsa, amma zai hukunta ka matukar ka yi zagi marar tushe ko cin mutunci. Wannan ne ya sa ba ya shiri da ’yan siyasa da kuma ’yan jarida. Har wadansu suke ganin shi ne silar da ya sa ake boye ayyukansa na alheri, ake kakaba masa ayyukan sharri a kullum.
 9. A tsawon mulkin marigayi Janar Sani Abacha na shekara hudu da rabi, sau daya ya kara wa man fetur kudi a Najeriya. A lokacin ne kuma ya kafa Asusun Tallafin Man Fetur (PTF) wanda ya danka shugabancinsa ga Janar Muhammadu Buhari. Hakika masana sun tabbatar da cewa wannan abu da Janar Abacha ya yi, shi ne silar samun farin jinin Janar Buhari saboda amanar da ya rike da kuma dimbin ayyukan da ya yi a karkashin asusun a lokacin mulkin Abacha, har kuma daga baya aka yi masa tayin shigowa siyasa tare da neman shugabancin kasar nan.
 10. Marigayi Shugaba Sani Abacha ya rasu a ranar 8 ga watan Yunin 1998. Kuma kafofin watsa labarai sun rika ruwaito zantuka daban-daban bisa silar rasuwarsa, abin da ake ganin makusantansa ne kurum za su iya fadar gaskiyar lamarin. Amma dai ana kyautata zaton guba aka sanya masa a abinci domin kawo karshen mulkinsa.
Hakika duk mai rai mamaci ne, don haka muna addu’ar Allah Ya gafarta masa, kuma Ya kyautata tamu zuwan kuma, amin
Sadik Tukur Gwarzo
08060869978