Da Dumi Dumi

Mazauna kan iyakar Seme na kuka da matakin gwamnati

Alhaji Zubairu Mele Abba Gana
Alhaji Zubairu Mele Abba Gana

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar nan inda jami’an tsaro da suka hada da Kwastam, da sojoji da na Hukumar Shige da Fice da sauransu suke gudanar da aikin tsaro na hadin gwiwa.

Kakakin Hukumar Kwastam ta Kasa Joseph Attah, wanda shi ne kakakin hadakar kan iyakokin kasar ne ya sanar da haka.

Aminiya ta ziyarci kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin da ke Seme domin bin diddigin halin da ake ciki inda ta ga tarin jama’a a zaune a kan iyakar, mafi yawansu direbobin manyan motoci da ke kokarin fita da kayayyaki ko  shigowa da su kasar nan.

Aminiya ta zanta da wadansu daga cikin direbobin inda suka ce ba su san da shirin gwamnati na daukar wannan mataki ba, domin da sun sani da ba za su taho ba, saboda zuwa yanzu ba su da tabbacin lokacin da za su bar wajen kuma duk guzurinsu ya kare.

Daya daga cikin shugabanin al’ummar da ke zaune a iyakar, Alhaji Zubairu Mele Abbagana wanda jami’i ne da ke yin fiton kayayyaki daga kasashen ketare zuwa Najeriya, ya ce wayewar gari suka yi suka tsinci kansu a wannan hali, “alhakin gwamnati ne ta kare kasarta da kan iyakarta, kuma mu ma hakkinmu ne mu taimaka mata mu ba da tamu gudunmawar domin kare martabar kasarmu da tsaron kasa. Amma ya kamata duk lokacin da gwamnati za ta dauki irin wannan mataki ta sanar yadda talakawanta za su shirya wa lamarin. A farkon matakin an rufe kan iyakokin ne kacokan babu shiga ba fita, amma daga bisani an sassauta inda ake barin matafiya masu cikakkun takardu su wuce ba a bari su dauki kaya. Halin da ake ciki mu da iyalanmu da muke zaune a kan iyaka muna cikin matsi, farashin kayayyakin masarufi sun yi tashin gwauron zabo, a baya muna samun kayan abinci da suka hada da kayan gwari, amma yanzu sai an kawo mana daga Kasuwar Mil 12 a Legas. Wani abin takaici shi ne yadda jami’an tsaron suka kama wata mota dauke da kayan miya suka kwace kayayyakin kuma suka zo suna sayar da su ga jama’a. A tunanina wannan ba daidai ba ne, a kwace kayan mutum kuma a sayar, wannan kayan abinci ne da babu haramci a kansu. Ina kira ga gwamnati ta yi la’akari da halin da talaka ke ciki a wannan yanki.”

ADVERTISEMENT

Haka wadansu da suka bayyana kansu a matsayin ’yan kungiyoyin manoman kayan gwari da ke yankin Yewa a Jihar Ogun sun yi zanga-zangar lumana a cibiyar ’yan jarida ta Jihar Ogun dauke da kwalayen da ke isar da sakonni daban-daban. Sun koka cewa jami’an Hukumar kwastam sun kama musu manyan motoci dauke da tumatir da attarugu wadanda suka kiyasta kudinsu a kan Naira miliyan hudu. Shugaban Kungiyar Manoman, Mista Timothy Eweoba ya ce kowace mota tana dauke da kwandon tumatir 250 da kudinsa ya kama Naira dubu biyu duk kwando, inda Hukumar Kwastam take sayar wa jama’a a kan Naira 200.

A martanin da ya yi kan ikirarin masu zanga-zangar, Kakakin Hukumar Kwastam ta Kasa, Joseph Attah ya musanta cewa kayan tumatirin da attarugun da hukumar ta kama a nan Najeriya aka shuka, inda ya ce jami’an tsaron hadin gwiwa da ke aikin na musamman a kan iyakar ne suka kama motocin dauke da kayayyakin a kan iyakar kasa, kayayyakin miyan da ya ce an yi fasakwaurinsu ne daga kasashen waje.

A wani bincike da Aminiya ta yi a kan iyakar zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami’an tsaron sun kama akalla mutum 65 da ke kokarin shiga ko fita daga kasar nan ta yankin Seme ba tare da takardu ba. Wata majiya ta ce mutum 15 cikinsu bakin haure ne da ke kokarin shigowa kasar nan ta barauniyar hanya wadanda bayan an kammala bincike a kansu aka kore su tare da yi musu kashedin cewa kada su kuskura su sake yunkurin shigowa Najeriya ba tare da takardu ba. A cewar majiyar ragowar mutum 50 din ’yan Najeriya ne da suka yi yunkurin ketarawa kasashen ketare ta barauniyar hanya ba tare da takardu ba, su ma aka juyo da su.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa gwamnati ta dauki tsauraran matakan ne a kan iyakokin kasar nan musamman a yankin Seme da Idiroko da ke iyaka da Jamhuriyar Benin bayan da hukumomin kasar Benin suke rikon sakainar kashi kan yarjejeniyar da ke tsakaninsu. Majiyar ta ce mahukuntar kasar Benin ba sa tabuka abin a zo a gani wajen kiyaye iyakar kasar, inda sakacinsu ke janyowa ake yawan fasakwaurin haramtattun kayayyaki da suka hada da miyagun kwayoyi da makamai da sauran kayayyakin da aka haramta shigowa da su kasar nan.

Zuwa yanzu dai hada-hadar kayayyaki da harkokin kasuwanci na yau da kullum sun tsaya cik a kan iyakar Seme lamarin da ya sanya al’ummar yanki shiga cikin damuwa.

Share