✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mazauna Kawo a Kaduna sun kashe mai garkuwa da mutane

Mazauna unguwar Kawo a jihar Kaduna sun kashe wani mutum da suke zargin mai garkuwa da mutane ne, kuma sun ce mutumin yazo unguwar ne…

Mazauna unguwar Kawo a jihar Kaduna sun kashe wani mutum da suke zargin mai garkuwa da mutane ne, kuma sun ce mutumin yazo unguwar ne da nufin yin garkuwa da wani mazaunin garin.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, a safiyar yau Litinin da misalin karfe 8 ne mazauna unguwar suka samu rahoton cewa, wasu masu garkuwa da mutane su uku sun shigo unguwar, inda suke da shirin yin garkuwa da wasu mutanen yankin.

Mazauna unguwar sun rufe duk hanyoyin shiga unguwar, sun fatattaki wadanda ake zargin tare da kashe mutum daya daga cikin ‘yan garkuwan.

A lokacin da jami’an `yan sanda suka ziyarci yanki, an yi kuskuren harbin wani mai sayar da lemu tare da jikkata wasu da dama.