Da Dumi Dumi

Mbappe ya cire hotunan Cristiano Ronaldo da ya lika a dakinsa

Mbappe ya cire hotunan Cristiano Ronaldo da ya lika a dakinsa

Kylian Mbappe dan kwallon Faransa da kuma kulob din PSG ya cire daukacin hotunan Cristiano Ronaldo da ya lika a dakinsa, inda ya maye gurbinsu da nasa.

Dan kwallon ya yi haka ne ganin yadda shi ma ya kawo karfi a fagen kwallon kafa, inda a bara ya samu nasarar lashe Kofin Kwallon Kafa na Duniya a Rasha, baya ga gasar rukuni-rukuni ta Faransa.

Rahotanni sun ce Mbappe tun yana karami babu dan kwallon da ya fi kauna irin Cristiano Ronaldo, amma bayan da ya lashe Kofin Duniya a bara ya rika canja ra’ayi game da wasu al’amurra ciki har da cire daukacin hotunan Ronaldo da ke dakinsa, inda ya maye gurbinsu da nasa.

Dan kwallon ne da kansa ya sanar da haka a shafin sadarwarsa ta Instagram a ranar Talatar da ta wuce.

Mbappe dai yana daga cikin matasan ’yan kwallon da tauraruwarsu ke hasakawaa duniya, ganin yadda manyan kulob a sassan duniya suke zawarcinsa ciki har da na Real Madrid da ke Sifen.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya