✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke faruwa da kasata Najeriya?

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga Mayun bara. Al’umma na cike da farin ciki da murna tare da…

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga Mayun bara. Al’umma na cike da farin ciki da murna tare da kyakkyawan fatan cewa al’amura za su inganta, canji ya samu, kasa za ta dawo cikin hayyacinta. Bayan tabarbarewar al’amura a karkashin mulkin jam’iyyar PDP na shekara goma sha shida.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari mai taken canji ta bayyana kudurinta da manufofinta a kan mayar da kasar nan bisa kyakkyawar turba ta asali da kuma ceto tattalin arzikin kasar da ya durkushe.  Ga duk inda al’adar gyara take a duniya, tana kunshe ne da wahalhalu da matsaloli da suke kasancewa tarnaki ga cimma buri. Dole ne a runtse idanu a ratsa wannan runtsi domin kaiwa ga tudun-mun-tsira. Allah Ya ce: “Ga dukkan tsanani akwai sauki.” A dai kara hakuri nasarar Allah za ta zo, nesa ko kusa.
Tabbas wannan gwamnati ta gaji tarin matsaloli masu sarkakiya da yawa, da suka shafi tafiyar da mulkin kasa cikin jin dadi da walwala. Ta karbi mulki a daidai da lokacin da danyen man fetur ya fadi warwas a kasuwar duniya, wanda shi ne babbar hanyar samun kudi ga kasar nan don tafiyar da gwamnati.
A yau an wayi gari, duk inda ka je birni ko kauye zance daya ake “Kan yadda gwamnati ke tafiyar da mulkinta.” Mutane na ta kukan talauci da fatara, yunwa da kuma tsadar kayan abinci da na masarufi. Mutumin da ke sayen buhun masara ya koma yana sayen tiyoyi. Mai sayen tiyoyi ya dawo yana sayen garin kwaki idan ya samu sukunin hakan!
A baya kafin zuwan wannan gwamnati kididdiga tana nuna talakan kasar nan na rayuwa a kasa da Dala daya a lokacin Dalar tana Naira 160. A yanzu idan talaka zai auni masara ko gero sai ya cire Naira 400 kafin a ba shi kwano guda. Saboda Allah mutumin da Naira 160 ta gagare shi, ina zai samu Naira 400? Allah Ya kawo mana saukin wannan hali, masu hannu a kan musguna wa talaka Allah Ya yi maganinsu.
Kafin watan azumin bana Shugaba Buhari ya bayar da umarnin fito da tan 10,000 daga rumbun kasa domin sayarwa ga talakawa cikin farashi mai rahusa. Amma har yanzu babu wanda ya san inda aka kwana a kan batun!
’Yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya daidaita da aka tsugunar a sansanonin da dama a Arewa maso Gabas kullum suna kukan yunwa ba abinci, ba magunguna suna cikin kuncin rayuwa dadi ga wanda suka tsinci kansu. Ga shi gwamnati na ware makudan kudi don tallafa musu, amma ka rasa inda abin ke makalewa.
Ma’aikata na kukan rashin albashi a kan lokaci, musamman a jihohi. Ga zunzurutun kudi Gwamnatin Tarayya na tura wa gwamnoni a kan su biya albashi, amma abin ya faskara! Har yanzu akwai dubban matasa da ke ci gaba da zaman kashe wando, da rashin sanin yaya makomar rayuwa za ta kasance.
A baya ana ganin rashin aiwatar da kasafin kudin bana, mai cike da sarkakiyar gaske a kan lokaci shi ne ya zama tarnaki dangane da fara aiwatar da ayyukan raya kasa. To amma yanzu watanni masu yawa sun shude bayan amincewa da kasafin a matsayin doka, har yanzu ba ta canja zane ba!. Tazara tsakanin mawadata da talakawa ta kara nisa mai yawan gaske. Talaka ya gane cewa shi talaka ne!
Mutane da daman gaske na zargin cewa makusantan Shugaba Muhammadu Buhari na da hannu dumu-dumu wurin kawo cikas kan aiwatar da wasu manufofinsa. Wanda a wani bangaren “Biri ya yi kama da mutum.”
Duk da kasancewar tun farkon hawansa ya yi jan kunne ga makusantan nasa a kan ba sani ba sabo, to amma wadansu sukan bi wasu hanyoyin domin azurta kansu ba tare da sanin Shugaban ba. Shakka babu gwamnatin nan na da tarin makiya na sarari da na boye, na kusa da na nesa, amma da yardar Allah hakarsu ba za ta cimma ruwa ba.
 Muna fata Shugaba Muhammadu Buhari zai kara sanya idanu a kan wadanda ke wakiltarsa domin yi wa tufkar hanci.
Alhamdulillah, kamar yadda tsaro ya samu da kwanciyar hankali cikin kankanen lokaci a kasar nan, Insha Allahu komai zai inganta. Mu dai talakawa mu ci gaba da addu’a da tausaya wa junanmu tare da gyara halayenmu.
Wahalar da muka sha ta tsawon shekaru don samun canji ba za ta ta fi a banza ba. Duk mai hannu a kan musguna wa talakawan kasar nan a cikin wannan gwamnati ya kwana da sanin “Allah na nan a madakata”.Sannan addu’armu za ta yi aiki a kansa, tun a duniya zai ga sakamakonsa, kafin komawa ga Allah don hukunci.
Muna yi wa Shugaba Muhammadu Buhari fatan samun nasara a kan manufofinsa ga kasar nan, Allah Ya yi masa jagora, Ya ba shi ikon sauke wannan nauyi.
Za a iya samun Injiniya Jibril Abdul Daura a wadannan lambobi 08038997861,08022997043