✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke faruwa tsakanin Shugaba Buhari da Mataimakinsa?

Sannu a hankali tsare-tsaren tafiyar da mulki da suke gudana a ofishin Shugaban Kasa da sauran ma’aikatun Gwamnatin Tarayya bayan dawowar Shugaba Muhammadu Buhari da…

Sannu a hankali tsare-tsaren tafiyar da mulki da suke gudana a ofishin Shugaban Kasa da sauran ma’aikatun Gwamnatin Tarayya bayan dawowar Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo kan karagar mulki a karo na biyu ranar 29 ga Mayun da ya gabata, sai daukar sabon salo suke, suna haddasa ka-ce-na-ce a gwamnatin. Wadansu ’yan kasa kuma na ta ci gaba da yin fassara iri-iri. Wadansu na cewa ana yin ne don zaben shekarar 2023, wadansu kuma na cewa ba don haka ba ne.

Shi kuma Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Osinbajo da al’amarin ya fi shafa kuma ake tunanin yana son ya gaji Shugaba Buhari, daidai da rana daya bai taba furta yana kwadayin neman shugabancin kasar nan ba a shekarar 2023, in Allah Ya kai mu.

Kafin zaben 2019, an zargi Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo lokacin da ya rike kasar nan, lokacin da Shugaba Buhari ya yi fama da matsanancin rashin lafiya da har yau ba a fada wa ’yan kasa kowace iri ce ba. Tun wancan lokaci ake zargin Mataimakin Shugaban Kasar da daukar da wasu matakan mulki da ake kallon Shugaba Buhari da mukarrabansa ba su ji dadinsu ba. Matakai ko kudirorin sun hada da yadda a ranar 14 ga Yulin 2016, Mataimakin Shugaban Kasar a matsayinsa na Mukaddashin Shugaban Kasa ya aike da sunan Alhaji Ibrahim Magu ga Majalisar Dattawa don neman amincewarta ya zama tabbataccen Shugaban Hukumar EFCC, batun da bayan tsawon lokaci Majalisar Dattawar ta sa kafa ta shure.

Kuma a cikin watan Fabrairun 2017, Farfesa Osinbajo ya sake rubuta wasika ga Majalisar Dattawa yana neman ta amince a nada Mai shari’a Walter Samuel Onnoghen a matsayin Babban Jojin Najeriya. Sai a watan Agustan 2018, Farfesa Osinbajo ya sallami Darakta Janar na Hukumar DSS Alhaji Lawal Daura daga mukaminsa bisa zargin ya tura jami’ansa sun kutsa kai a cikin harabar Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja. Kazalika an zargi Mataimakin Shugaban Kasar da bada umurnin a rusa tare da yin garambawul a sashen yaki da fashi da makami da sauran miyagun laifuffuka na Rundunar  ’Yan sandan Najeriya (SARS), a daidai lokacin da wadansu ’yan kasa suke ganin SARS tana iyakacin kokarinta. Duk an yi zargin Farfesa Osinbajo ya zartar da wadancan kudirce-kudirce ne ba tare da taba alli ba daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Bayan zaben bana, a ranar 16 ga  Satumban da ta gabata, Shugaba Buhari ya umarci Mataimakinsa ya rika neman izininsa kafin zartar da duk wani abu a kan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da suke karkashin kulawarsa. Wadannan ma’aikatu da hukumomi sun hada da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Kula da Jin Dadin Al’ummomin kan Iyakokin Kasar nan (BCDE) da Cibiyar Nazarin Muhimman Bukatu ta Kasa (NIPPS) da ke Kuru kusa da Jos, wato NIPSS da Hukumar Kula da Iyakokin Kasar nan.

Sauran hukumomin da suke karkashin kulawar Mataimakin Shugaban Kasar da umarnin ya shafa, sun hada da Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Neja-Delta da ke mallakin rukunin gwamnatocin kasar nan uku, wato Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi.

Kafin bayar da wancan umarni, Shugaba Buhari ya rusa shugabancin Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa da ke karkashin Mataimakinsa, tare da maye gurbinsa da kafa Majalisar Bada Shawara kan Tattalin Arziki da za ta rika mika rahoto kai-tsaye ga Shugaban Kasa.

Shugaban Kasar yana hutu mako biyu a Landan ne aka ji a ranar 4 ga  Nuwamban nan ya sa hannu a dokar da za ta kara samar da kudaden shiga a matsayin haraji daga kamfanoni masu hako danyen man fetur din kasa. Wannan aiki da ya yi, ya kara jawo ka-ce-na-ce a tsakankanin lauyoyi da ’yan gwagwarmaya da ’yan hamayya, a kan Shugaba Buhari bai amince da Mataimakinsa ba, tunda yana hutu kuma a kasar waje zai gudanar da irin wancan gagarumin aiki.

Daga bisani hakarkari sun kwanta, bayan da mafi yawan masana kan fassarar tanade-tanaden tsarin mulkin kasar nan suka ce bisa ga tanadin sashe na 145, na kundin, ba wani laifi da Buhari ya yi don ya sa hannu kan waccan doka walau a lokacin yana hutu ko yana wata kasar duniya. Kasancewar tanadin wancan sashe ya ce sai idan Shugaban Kasa ko Gwamnan jiha za su yi tafiya hutun da ya zarta kwana 21, kana za su mika ragamar mulki ga mataimakansu, alhali a wancan tafiyar ta Shugaban ba ta wuce ta kwana 17, ba.

Kwana hudu bayan da Shugaba Buhari ya sa hannu a kan wancan doka, wato a ranar 7 ga Nuwamba, sai kuma ofishinsa ya raba takardar sallamar mukarrabai 35 daga cikin sama da 80 da suke ofishin Mataimakinsa. Da wannan mataki da wadancan na baya da Sugaban ya dauka sai wuta ta kara ruruwa kan zargin cewa lallai zaman doya da manja ake yi a tsakanin Shugaba Buhari da Mataimakinsa, har ta kai mutane irin su Mista Yinka Odumakin Kakakin Kungiyar Yarbawa zalla ta Afenefere ya shawarci Mataimakin Shugaban Kasar da ya gaggauta sauka daga kan mukaminsa, yana mai cewa abubuwan da suke faruwa suna nuni da ba  ya da wani amfani a gwamnatin. Zarge-zargen da Fadar Shugaban Kasa ta yi ta musantawa.

Shi kuwa Shugaba Buhari da ya dawo kasar nan a ranar Juma’ar da ta gabata da dare ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, bayan kammala hutun nasa, mamakinsa ya bayyana wa manena labarai kan irin yadda ake juya gyara-gyare da tsare-tsaren gwamnatinsa a kan kabilanci da siyasa. Yana mai cewa, “Kowa ya san gwamnati ta kara kirkiro sababbin ma’aikatu, lamarin da ya bukaci a yi gyare-gyare, wanda shi mu ka yi aka mayar da batun na kabilanci da siyasa.”

Makamantan irin wadannan zarge-zarge da fito-na-fito aka rika samu tsakanin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da Mataimakinsa Atiku Abubakar a wa’adinsu na biyu, al’amarin da ya kasance kotuna suka rika raba su. A cikin rashin waccan jituwa tsakaninsu (da ta shafi mabiyansu da jam’iyyarsu ta PDP) suka bar mulki a shekarar 2007, inda za a iya cewa an rabu tsiya-tsiya, ba su dawo sun sha inuwa daya ba, sai a dalilin zaben bana.

’Yan kasa na yi wa Buhari da Mataimakinsa kallon dattawa a harkokin siyasar kasar nan, inda ake ganin suna tafiyar da mulki cikin fahimtar juna. Don haka sai su yi hattara da na kusa da su da za su hada su don neman biyan bukatarsu, musamman yanzu da Kakakin Kungiyar Afenifere Mista Yinka ya fara kiran Osinbajo ya sauka, nan gaba kadan kuma sai wata kungiyar ta ’yan Arewa ko na kusa da Shugaba Buhari su ce ya kori Mataimakinsa.