✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke kawo Amosanin ka?

Wai shin likita me ke kawo ciwon amosani ne a kai? Mene ne magani? Don an ce min ba a rabuwa da shi. Kuma wai…

 Yadda Amosanin Ka ke cin gashiWai shin likita me ke kawo ciwon amosani ne a kai? Mene ne magani? Don an ce min ba a rabuwa da shi. Kuma wai da gaske ne idan aka takura masa da magani yana saukowa ya taba lafiyar ido?
Daga Abu Ammar, Kano
Amsa: Da farko dai ya kamata da kai da sauran masu karatu su fahimta cewa amosanin kai ba ciwo ba ne, wato ba cuta ba ce wadda wata kwayar cuta ke iya sa wa. Kamar matsalar saba ta sauran fatar jiki da wasu suke ganin kamar ciwo ne, amosani shi ma saba ce da kan faru a fatar kai wadda take karkashin suma. To idan tana barbashewa za a ga fari-fari na zuba kamar gari, musamman idan an zo taje kai ko kitso ko an zo yi wa mutum aski.
Bari mu fara dora bayanin a kan ita kanta fatar jiki tukuna, sa’annan ka gane cewa ba matsalar da za ka damu da ita ba ce sosai. Dama fatarmu canzawa take daga lokaci zuwa lokaci, kusan a ce wata-wata, dangane da irin abinci da muke ci da yanayin gari wato, zafi ko hunturu ko rani ko damin, da irin abin da muke shafa mata da kuma yawan shekaru, wato tsufa ko kuruciya. Duka fatar kowa tana son abinci mai lafiya isasshe, mai dauke da sinadarin abinci mai gina jiki wato protein, wanda daga shi ne fatar kan sarrafa sinadaran keratin da collagen da elastin, wadanda su ne ginshikan ita kanta fatar. Sai kayan marmari masu dauke da bitaman masu sa fata sheki da walwala. Akan iya samun wasu sinadaran ma a man da muke shafawa, wanda shi ma fata kan tsotse su idan an shafa. Don haka za ka ga fatar wadanda suka faye samun wadannan irin abinci da mai daban da ta wadanda ba su cika samun hakan ba kuma a iya cewa fatarsu ta fi lafiya kuma ta fi rashin nuna matsaloli.
Dangane da yanayi kuma wasu fatarsu ta fi son zafi, wasu kuma ta fi son yanayin danshi, a wasu kuma ta fi son yanayin sanyi. Babu fatar da ke son busasshen yanayi irin na hunturu. Misali, shi ya sa kusan kowa yakan samu matsalar fata a wannan lokaci, tun daga kaushi zuwa faso zuwa saba zuwa tsagewar lebe, zuwa waskane, har zuwa amosanin ka.
To amma duk da cewa amosani ba ciwo ba ne, yana daya daga cikin abin da kan sa mutane da yawa damuwa musamman ma mata, don haka dole a saurari mai korafin wannan matsala. Matsalar kan shafi kusan rabin mutanen duniya, ba bambanci a tsakanin jinsinan duniya.  Wasu lokuta yakan sa kaikayi, mutum ya yi ta sosa kai, wanda wannan ma idan a cikin mutane ne sai kunya ta fara kama shi. Idan ana sosawa kuma barbashin kan biyo kai a gan shi a saman suma ko a kafada.
A gaskiya babu abin da zai warkar da amosanin ka, tun da ba ciwo ba ne, sai dai abin da zai rage shi. Kamar yadda muka fada a baya, yanayin abinci da na wuri suna taimakawa, haka ma man wanke kai wadanda ga su nan birjik a kasuwanni da manyan shaguna ba sai a kyamis ba. Da mutum ya je ya ce a ba shi maganin shamfo na amosani za a ba shi mai kyau. Mutane da dama sun fi ganin amfanin wani wai shi head and shoulders fiye da sauran. A mafi yawan lokuta da an fara amfani da shi za a fara ganin saukin barbashewar suma da kuma kaikayi. Ba wai hana fatar marmashewa yake ba, a’a yakan ba fata laushin da ba za a san lokacin da ta canza ba, tunda dole ne duk bayan ’yan makonni sai ta sama ta marmashe ta karkashi ta tofo. Ka ga ke nan babu tabbas din idan ka daina amfani da shi ba zai dawo ba.
Babu kanshin gaskiya game da cewa idan kurar kan ta amosani ta sauko ta shiga ido tana illa ga lafiyar idon.
Sai mai tambayar, cewa wai shin likita me ke faruwa ne da ni? Da na ci abinci ko da ban yi wani aiki ba sai nan da nan na sake jin wata yunwa. Me yake kawo haka?
Daga Mustafa H. Kano
Amsa: Wasu ma sukan ce ai olsa ce take sa saurin jin yunwa, wanda ba haka ba ne, sai dai ma rashin abinci a ciki ya kawo yunwa. Yunwa daban, rashin abinci a ciki daban. Sau da yawa mutum zai ci abinci amma ya ji kamar ya lasa. A likitance dan abin da ya ci zai zauna a cikinsa na wani dan lokaci kuma zai masa amfani ya ba shi kuzari na wani dan lokaci. Wasu sai sun ci mai yawa suke koshi, wasu kuma akasin haka, amma dai ya kamata a gane a kimiyyance koshi fa ba a yawan abinci yake ba, a abubuwan da aka hada a abincin da su ne komai kankantarsu. Idan aka samu abinci mai dauke da kowane irin kayan ci a lokaci guda aka ci, da wuya a samu matsalar saurin jin yunwa.
Ni ina ganin kuma har da al’ada. A al’adarmu mun saba loda kwano da abinci kala biyu zuwa uku a ci a sha ruwa, kuma duk da haka wasu sukan ji basu koshi ba, amma a al’adar wasu akan samu abinci akalla kala biyar zuwa sama (kusan dai kamar yadda muke yi da azumi) a lokaci guda kuma kowanne dan kadan ba da yawa ba. Akan samu dan ganye da wani abu daga cikin kayan marmari, da wani dan nama ko kifi ko kaza, a kan sauran abin da ya samu. Ko yaya mutum ya ci kadan-kadan daga cikin wadannan ya sha ruwa zai ji daidai.
Ban da irin cimakar azumi kuma bari na kara ba ka wani dan misali, idan ka taba tafiya a jirgin sama, inda za ka ga idan lokacin abinci ya yi akan kawo wasu ’yan kananan robobi dauke da abinci kala-kala ga shi kansa abincin ga ganyayyaki ga daya daga cikin kayan marmari, a kawo wata ’yar gurasa ko burodi da abin shafa masa mai lafiya, a kawo dan ruwan lemo, a kawo ruwan sha, a kawo dan shayi. Da farko idan mutum ya ce da girman robobin zai auna abincin sai ma ya yi tsaki amma idan ya gama ci ina tabbatar maka sai barci.

LAFIYAR MATA DA YARA

Me ke kawo wa yara da ba su wuce kwana arba’in ba yawan amai ne?
Daga Muhsin, Katsina
Amsa: Akwai abubuwa da dama da kan sa wa jarirai yawan amai. Na farko dai shi ne shigar kwayoyin cuta cikin ciki ta hanyar ba su gurbataccen ruwa, ko ruwa mai kyau amma ta bulumboti ko kofi gurbatacce, domin idan ruwan nono kawai ake ba jariri, da wuya kwayoyin cuta su shiga cikinsa. Yawanci yawan amai a irin wannan yana kuma hade da yawan bayan-gida wato gudawa.
Akwai kuma wadanda za su iya samun kwayoyin cutar tun a cikin mahaifiyar, amma yawanci wannan ba amai da gudawa sukan kawo ba, yawanci zazzzabi da amai sukan kawo a ’yan kwanakin farko na haihuwa. Wadanda suke zuwa a kwanaki arba’in yawanci wadanda jariri ya kwasa ne ko dai a gidansu ta hanyar shakar gurbatacciyar iska (mai dauke da kwayar cutar sankarau). Misali, kamar ranar suna idan mutane sun cika gidan, ko a wurin wanzamai idan an yanke masa beli, ko ta cibi idan ba a gasa masa ita da kayan kashe kwayoyin cuta irinsu spirit. Wato dai kwayoyin cutar za su iya shiga ko ta hanci, ko ta makogwaro ko ta cibi ko ta mafitsara, idan uwa ba ta iya yi wa jariri tsarki ba sosai. To wadannan su zazzabi za su kawo da yawan amai.
Amma idan jariri yakan dade kafin ya yi bayan gida kuma yana yawan amai a kai-a kai, to a irin wannan hali a iya cewa akwai abin da ya toshe tsakanin tumbi zuwa uwar hanji. Jarirai da yawa ana iya haifar su da irin wannan matsala amma a kwanakin haihuwa na farko-farko ake gani ba a kwanaki arba’in ba.
Ko ma dai mene ne dai ba kai ne za ka tantance mene ne sababi ba, da ka ga jariri kwana daya kwana biyu yana ta amai, ka san ba lafiya kuma ka san inda za ka kai shi.
Wai shin dole ne wai sai an cire wa jariri beli zai yi lafiya ko dai fadar mutane ce kawai? Idan ba a cire ba me zai faru?
Daga Ghali, Bauchi
Amsa: A’a, a likitance ma ba a so, sai idan belin yana so ya zama matsala ta wurin sa minshari ko rashin fitar furuci sosai. A al’adance ne kawai ya zama kamar dole. Idan ba a cire ba babu abin da zai faru.