✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke kawo sandarewar hannaye?

Mene ne yake kawo sandarewar yatsun hannu, ko shi kansa hannun ya lauye ya rike gam? Daga Muhammad Goni, Yobe   Amsa: Wannan bayanin ya…

Mene ne yake kawo sandarewar yatsun hannu, ko shi kansa hannun ya lauye ya rike gam?

Daga Muhammad Goni, Yobe

 

Amsa: Wannan bayanin ya yi kama da wata alama da mukan kira da sunatetany a likitance, inda za a samu wuyan hannayen sun lankwashe amma tsintsiyar hannun a tsaye, ko kuma yatsu a dunkule a wasu lokuta. Wannanmatsala akwai abubuwa da dama masu kawota a likitance tun daga kankarancin wasu sinadarai a abinci (kamar sinadarin calcium da magnesium) zuwa shigar kwayoyin cuta jiki irinsu kwayar cutar Shan inna, wadda ita takan ma maida hannun shanyayye, zuwa kwayar cutar Sarke hakora, zuwa ciwon Makoko da sauransu. Duk wanda aka ga ya fara samun irin wannan alama dole a yi maza a kai shi Asibiti cikin gaggawa domin duk wadannan matsaloli da muka lissafa Asama masu samar da alamun, dole a yi maganinsa cikin sauri. Da an duba mutum an auna jini ana gane ko mene ne takamaimai sinadarin da babu, ko ciwon da ke akwai. Nan take za a ba da magani wanda idan aka dace an warkar da matsalar ke nan. Sai dai a sanar da maras lafiyan ga dalili, ga kuma hanyoyin da zai kiyaye dukuwar abin a gaba.

 

Jikina na yawan mini zafi a kowane lokaci musamman da safe idan na tashi daga barci. Shin ko hakan na nuni akwai matsala?

Daga Abdul Abdulhamid

 

Amsa: E, kwarai kuwa hakan na nufin sai ka je an duba ko akwai matsalar ko babu. Ba irin alamar da za a ce ba komai ba ce wannan.

 

Ina da matsala a cikina wadda da zarar na yi tafiya mai dan nisa sai na ji cikina ya kulle a gefe guda. Mece ce shawara?

Daga Usman BB, Sokoto

 

Amsa: In dai sai lokacin da ka yi tafiya mai dan nisa ne yake maka to ba matsala ba ce da za ka damu, sai dai kawai ka rage nisan tafiyar ko ka canza yanayin motsa jikin, misali ka hau keke maimaikon tafiyar kafa. Amma in dai haka kawai kana zaune ko kwance kana jin irin matsalar to shi ne za ka damu ka nemi mafita ta hanyar gwaje-gwaje kafin magani.

 

Na dade ina aiko da tambaya ba a amsawa. Tambayata akan abinda ke sa mutum tari ba dare ba rana. Sai ya nemi maganin majina amma ba sauki. Ina mafita?

Daga Yakubu Musa, Jega

 

Amsa: Idan ka ga ba a amsa tambayarka ba kusan yana nufin an sha amsa irinta ke nan a wannan shafi. Ba dole sai taka tambayar ba, in dai ka ga wata mai shigen taka ka karanta za ka karu. An sha fadi a nan cewa tari mai naci da ya ki tafiya mai shi sai ya je asibiti an tantance masa ta hanyoyin aune-aune da gwaje-gwaje da hotuna. Domin wani lokaci ya zamo shigar kwayoyin cuta ne kirji, wani lokaci ya zamo ciwon asma ne, a’a kai wani lokaci ma za a ga ai ciwon zuciya ne ya jawo tarin. Haka dai akwai dalilai da dama wadanda sai an duba ne za a tantance.

 

Ni kuma bayan gida nake da majina.

Daga Mudan Anchau

 

Amsa: Kaima dole sai an duba ka, musamman idan ka dade kana yi, amma idan na ‘yan kwanaki ne abin da ya fi kawo irin wannan shi ne ciwon atini wadda wata kwayar cuta ke sa wa har da gudawa, in dai haka ne to tsaftar abinci da abin sha, da ta hannaye ce mafita

 

Ni idan ina shan kankana ina taune har da kwallayen na hadiye domin an ce mini yana wanke koda. Ko hakan gaskiya ne?

Daga Rabi Rijiyar Lemo, Kano

 

Amsa: A’a ba wani abinci Malama Rabi mai wanke koda sai dai ko yawan shan ruwa. Yawan shan ruwa yana da alfanu ga koda sosai. Duk da cewa shi kwallon kankana kamar bai da kiba, akwai wasu abubuwa da kawai mutane za a gaya masu magana a titi a ce masu maganin wanke kaza ne su dauka su rika amfani da shi ba bincike.

 

Na san dabino da zuma na da amfani ga jiki. Ko shan su a kullum sau daya a rana na da wata illa?

Daga Mubarak Matazu

 

Amsa: E, ba matsala da wuya ya kawo maka wata illa in dai ba jibgarsu kake sosai ba, tunda dukansu su biyu akasari abin da ke cikinsu suga ne, yawan sha da yawa zai iya sa suga yayi yawa a jininka

 

Ni ina sana’ar dare sai asuba nake tashi sai in yi barcin da rana. Shin hakan ba laifi ga lafiyar jikina?

Daga Aminu Muhammad

 

Amsa: E, to jiki kam tabbas ba a yi shi domin aikin dare ba, an yi dare ne domin hutu, kuma haka ma aka tsara yanayin jikinmu. Dole ce take sawa ka ga ana aikin dare. To idan ya zama dole din, kamar idan ka fi ciniki da dare a iya cewa shi ke nan tunda agogin jikinka zai jirkita lokacin hutawar ta dawo rana maimakon dare. Wato idan ka saba kai da kanka za ka ga ko ba ka je wurin sana’ar ba da dare ba ka iya runtsuwa, amma da gari ya waye sai ka ji barci. To haka jikinka zai rika yi. Idan kuma ka sake dawowa kan barcinka na dare, sana’ar rana, nan ma jikinka zai sake jirkita agogon jikinka ka dawo barcin dare, amma shi ma da fari sai an dan sha wahala kafin abin ya dawo daidai.