Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Me ke sa gani bibbiyu?

Idan ina jin yunwa sai in ga abubuwa suna karkasuwa bibbiyu. Amma da na ci abinci sai in fara gani daidai. Ko wannan matsala ce?

Daga Babangida Sani, Kubwa

ADVERTISEMENT

Amsa: Duk da yake yunwa na iya sa gani ya dusashe, da wuya ta sa a rika gani bibbiyu. Ka san akwai bambanci a tsakanin gani bibbiyu da gani dishi-dishi. Idan ka ji ana maganar gani bibbiyu to da walakin. Gani bibbiyu alama ce ta matsala a tsokokin ido masu jujjuya idanu (muscles), ko madubin ido (lens) ko a bangon ido (retina) ko jijiyar ido (nerbe). Abin da ya fi bata madubi da bango da jijiyoyin ido da zai sa irin wannan yawanci shi ne ciwon suga. Abin da kuma ya fi jawo matsala ga tsokar da ke jujjuya idanun shi ne ciwon harari-garke. Don haka dai ga alama ba lafiya ba ne wannan yanayi da ka shiga, sai an binciki dalili.

 

ADVERTISEMENT

Idan zan yi tafiya mai tsayi kamar daga Katsina zuwa Kaduna sai kaina ya rika ciwo ina jin tashin amai. Nakan samu maganin ciwon kai in sha sai ya yi sauki. Shin hakan ba matsala?

Daga Hussaini Kadarko, Katsina

Amsa: Eh, ba matsala tunda ba kullum kake sha ba sai ka tashi tafiya. Da ma akwai mutane da dama irinka wadanda ba sa iya doguwar tafiya sai sun samu irin wannan matsala. Sai dai ban da maganin ciwon kai har da maganin tashin zuciya za ka iya zuwa wurin likita ya rubuta maka, ta yadda duk lokacin da ka tashi tafiya idan ka sha ba za ka ji wadannan alamu ba.

 

Ni kuma idan na yi gudu sai kaina ya yi ta mini ciwo kafafuna su yi ta tsami. Ko hakan matsala ce?

Daga Nasir, Bauchi

Amsa: Duk da yake gudu zai iya sa ciwon kai da ciwon cinyoyi idan aka gama, amma dai da jiki ya saba abin yake tafiya. Za ka iya dan shan maganin ciwon kai da ciwon jiki domin ciwon ya lafa bayan an gama motsa jikin. Amma idan kana yi kullum ko jefi-jefi jiki ya saba amma matsalar ta ki tafiya to watakila kana wuce kima ko kiyasin motsa jiki wanda jikinka zai iya dauka. Ana so a rika yin sassarfa ko tafiyar sauri ta mintoci 30 ko gudu na mintoci kamar 20 a rana. Duk abin da ya wuce haka zai iya sa ka rika jin irin wannan

 

Na tashi daga barci sai na ga kafafuwana sun kumbura har zuwa idon sawu. Na dai kasance ina da jiki. Ko hakan matsala ce?

Daga Usman Kawo, Kano

Amsa: Eh, wannan ba lafiya ba ce Alhaji Usman sai ka je an binciki dalili.

 

Ina fama da ciwon gwiwa ne sai wata ta ce in sha maganin ampiclos. Ko hakan daidai ne?

Daga Zuwaira Musa Wuye

Amsa: Duk da dai ba ki zayyana cewa maganin ya yi aiki ko bai yi ba, wannan ba daidai ba ne, in dai wadda ta fada miki hakan ba malamar aikin lafiya ba ce.

 

Ni idan rana ta yi ko a wurin aiki ne sai in ji barci, har sai na dan samu wuri na huta. Ko hakan na nuni da wata matsala ce?

Daga Sa’du M.B

Amsa: A’a ai kowa a yini yana da dan lokacin da agogon kwakwalwarsa (circadian rhythm) yake nuna masa cewa lokacin hutawa ya yi. Kawai sai a ji kasala da alamun barci a wannan lokaci. Ko an ci abinci ko ba a ci ba idan lokacin ya zo mutum zai ji sai ya dan samu wuri ya dan huta kafin ya dawo daidai, koda kuwa bai yi barci ba idan ya dan huta jikin zai ware. Don haka ba wata matsala ba ce.

 

Ni allura aka yi mini a mazaunai, bayan wata uku sai wurin ya tashi da zogi da zafi. Ko me zan sa a wurin?

Daga Rabi A. Rijiyar Zaki

Amsa: A wasu lokuta akan yi rashin sa’a wurin da aka yi allura ya rika tashi da zogi loto-loto. A wasu lokuta ma ban da zogi wurin kan kumbura ya ja ruwa ya yi diwa. Wannan diwa za ta iya sa zazzabi a jiki, wanda sai an zuke diwar zai daina. Don haka idan zogi ne kawai ba kumburi ba zazzabi ba komai maganin zogi kawai ya wadatar. Amma idan akwai kumburi a wurin da zazzabi a jiki jefi-jefi abin ya fi karfin maganin zogi.

 

Wasu lokuta idan ina magana sai in ga hannayena suna karkarwa. Shin wannan wata matsala ce?

Daga Anthony Atama, Nasarawa

Amsa: Eh, a wasu lokuta akan samu haka idan mutum yana magana a wuri na bakunta ko a wurin taron jama’a masu dan yawa. Wannan ba wata matsala ba ce. Amma idan ya kasance yana faruwa a lokacin magana cikin mutanen da aka sani ne, kamar abokai to akwai matsala sai an je an binciki dalili.

 

Marainana sukan daure su yi sama su sa mini zafin ciki da jiki. Ko me ke sa haka?

Daga Malam Sanda, Legas

Amsa: Abubuwa biyu zuwa uku za su iya kawo irin wannan matsala, akwai matsalar murdewar marainan akwai kuma matsalar shigar kwayoyin cuta, akwai kuma wasu matsalolin da su kuma a jikin marainan a kan same su kamar kari ko kumburi da sauransu. Mai samun irin wadannan alamu bai ga ta zama ba, sai ya je an binciki dalili, domin matsalolin maraina ba matsalolin wasa ba ne suna iya sa a yi asarar barin da ake jin ciwon, ya rage saura bari guda kawai ke aiki.

 

Ni an mini allura ce a saman tafin kafa na kwana biyar sai wurin ya yi baki. Wadansu sun ce wai tautau ne. To ko akwai magani?

Daga Muttaka Ijora, Legas

Amsa: Eh, a wasu lokuta idan aka dade ana soka wa wani wuri a jiki allura baki yake a bakaken mutane ko a ga ja a fararen mutane. Wato jijiyar wurin ce ke zubar da jini ta ciki a karkashin fata sai ya sa wurin baki. Yana daukar lokaci kafin wurin ya warke sarai. A wadansu yakan ma ki warkewa ya zama kamar kuna. Ko ma dai yaya ya yi maka, za ka iya samun asibitin da ke da likitan fata ya ga wurin, ya ga ko akwai abin da za a iya ba ka domin ya baje.