✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ke sa idanu su yi ja ne?

Kuma ko akwai maganin da zai sa su washe su koma farare? Amsa: Akwai abubuwa da dan dama da ke kawo jan idanu, tun daga…

Kuma ko akwai maganin da zai sa su washe su koma farare?
Amsa: Akwai abubuwa da dan dama da ke kawo jan idanu, tun daga yanayi na halitta, zuwa shigar kwayoyin cuta zuwa shigar wani haki idanun, zuwa shaye-shayen kamar na sigari da na tabar wiwi, zuwa ciwon gilakoma da sauransu da dama. To idan mutum yana da daya daga cikin wadannan dole sai sun tafi kwayar idon za ta yi haske. Magani daya da zai sa jan ido ya baje shine irin wanda shigar wani abu kamar sabulu ko yaji ko haki, ko wani datti ya kawo shi. Shi irin wannan akwai maganin digawa wanda da an sa, jan zai baje. Yana aiki ne kamar maganin kaikayin jiki na piriton. Wani lokaci ma ko piriton din aka sha ba a sa na digawa ba zai washe.
To amma idan mutum ba haka aka haifeshi ba, ba kuma shaye-shaye yake ba, ba kuma wani abu ne ya shigar masa idon ba, ya ga ido na yawan ja, haka kawai, kuma yana yawan ciwo, to dole ya je a auna idon a tabbatar ba ciwon gilakoma bane, mai sa makanta.

Wai me ke sa tafin kafar mutum ya rika yin digo-digon baki ne. Shin hakan na nufin wata matsala ne?
Daga Abdullahi, Abuja

Amsa: Wani lokaci zubar jini a karkashin fata, musamman a masu yawan tafiyar kafa zai iya sa karkashin fatar ya yi digo-digon baki ko ja. A wasu masu shan sigari ma, wani sinadari baki-baki kan taru a a karkashin fatar lebbansu da tafukan hannaye da na kafa, ya yi digo-digo.

Shin kwayar tramadol za ta iya jawo wa mutum ciwon farfadiya?
Daga Zahraddeen, kankara

Amsa: E, duk wata kwaya da ke aiki a kwakwalwa za ta iya haddasa wannan matsala ga mai sha. Amma ya danganta da karfin kwakwalwar.

Ni likita ina jin kamar kiyashi na bina ne a jiki, amma idan na duba sai na ga ba kiyashi bane. Shin akwai matsala kenan?
Daga Isa, kiru

Amsa: E, akwai matsala, ba lafiya bace jin irin wannan. Sai ka je asibiti an binciki dalili.

Ni kuma muryata ba ta fitowa sosai. Shin hakan na nufin akwai matsala?
Daga Aminu, Suleja

Amsa: E, idan daga baya abin ya sameka, ba a haka aka haifeka ba, dole ne ka je a duba ko akwai matsala ko babu. Likitocin hanci da wuya da kunne sune za su iya tantancewa, kamar a asibitin kunne kenan.

Shin da gaske mutum zai iya daina magana? Yaya abin yake?
Daga Raheena, Kano

Amsa: E, akwai cutukan da za su iya illata jijiyoyin laka na harshe ko na makogaro, wandanda su ke sarrafa furuci. Wadannan cutuka sun hada da bugun jini a kwakwalwa, wanda ya fi haddasa mutuwar barin jiki. Sai kuma buguwa kamar ta hadarin mota, da ciwon sankara na makogaro, wanda ya fi kama masu shan sigari.

Ni kuma ina yawan samun rashin jin dadin jikina. Na je asibiti an ce ina da stress da yawan kitsen cholesterol. Me hakan ke nufi? Kuma za su iya rabuwa da ni?
Daga Maman Sadik, Zariya

Amsa: Abinda ake nufi da stress sh ine rashin samun hutu. Hutu daga kujuba-kujubar gida, kamar ta girki ko ta yara; ko kujuba-kujuba ta wurin aiki, ko ta wata damuwar rayuwa daban. To idan mutum ya rage wadannan kujuba-kujuba, kamar ta neman masu taya aikin gida, ko ta rage yawan kwanaki da awoyin zuwa aiki, ko ma ta canza wurin aikin idan rage awoyin ba zai yiwuba, to zai samu sukuni, ya ji rayuwarsa ta dawo sabuwa, ya rika samun nishadi.  Shi ma kitsen cholesterol yana da alaka da stress, domin mutanen da ba sa samun hutu sun fi ciye-ciye, sun fi cin abinci iri-iri. To kayan maiko ne dai da kitsen nama mutum zai rage idan yana so wannan na’uin kitse ya ragu a jininsa. Sai motsa jiki kamar na tafiyar kafa ta mintuna 20 zuwa 30 a yawancin ranakun mako.

Shin da gaske ne duk mai shan ruwan tapioca ‘ya’yan da zai haifa ba za su yi kwari ba?
Daga Tukur, Kwasara

Amsa: To in dai tapioca ta rogo da aka fi sani ce, babu kanshin gaskiya a wannan zance.

Me ke kawo tsagewar wurin bayan gida, ta yadda idan mutum ya zo tsuguno kamar an sa barkono a wurin?
Daga Ibrahim, Jos

Amsa: Wannan matsala da ake kira anal fissure a likitance, yawanci taurin bayan gida ne ke kawota. Yadda za a rage taurin bayan gida kuma mun sha maganarsa a nan. Akwai magungunan da za a iya ba mutum na rage zugi da sa wurin saurin warkewa idan aka ziyarci asibiti.

Ni hadari na yi, na ji ciwo a ka. Sai wurin ya daina tsiro da gashi. Shin akwai maganin da zai sa gashi ya tsuro a wurin?
Daga Aminu Lawal

Amsa: E, kwarai akwai magani a asibitin fata, ko wurin likitan fata a babban asibiti wanda ke da bangaren duba fata. Sai dai ya danganta da ko kwayoyin halittar tsuri da suma a wurin suna nan ko sun mutu.

Me ya sa idan aka fasa kurajen fuska sai wurin ya yi tabon baki, kuma ya ki tafiya?
Daga Mubarak Hussaini

Amsa: E, haka ne, shi ya sa ba a cika so mutum ya rika fasa kurajen da hannunsa ba, don gudun tabon, sai dai ya sha magani ko ya sayi na shafawa, dangane da tsananin matsalar. Su kurajen idan na shafawa wanda ake saya a kyamis ba su yi aiki ba, akan dangana ga likitan fata ne, wanda shi kuma zai rubuta masu karfi, wadanda watakila ma su fitar da tabon.

Ina da wani matsanancin ciwon kai wanda kafin ya fara sai na fara gani dishi-dishi tukana. Mene ne magani?
Daga Shamsu, Gwarzo da Hauwa Imam da Umar, Ankpa

Amsa: In dai magani kuke nema a wannan fili bai wuce muce ka sha panadol ba. Amma kai daga jin irin wannan ciwon kai ai ka san ya fi karfin panadol. Don haka sai dai shawara. Watakila sai kun shigo birni a babban asibiti an muku aune-aune da gwaje-gwaje, har ma da hoton kan watakila, kafin su gano ko mene ne.

Da gaske ne cin gyada yana iya harzuka hawan jini da kurajen fuska?
Daga Maman Zuhra da Sadi dahiru, Marabar Jos.

Amsa: E gyada mai gishiri sosai za ta iya harzuka hawan jini, amma banda maras gishiri sosai. Haka nan kuma za ta iya harzuka kurajen fuska saboda maikonta

Da yaushe ne mai ciwon tabin hankali zai daina shan magani?
Daga Salihu Jada

Amsa: Lokacin da likitocin da suka dora shi a kan maganin suka ga maganin ya yi aikinsa, wato maras lafiyan ya dawo hayyacinsa. Amma ba abin mamaki bane a wasu, da an tsayar da magani alamun ciwon ya dawo, don haka a wasu ba lokacin tsayarwa.