✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya kamata a bude baki da shi?

A yanayi nan zafi, wanda kan sanya ruwan jikin mutum saurin karewa ta hanyar zufa, dole mai azumi da fari sai ya guji rana. Muna…

A yanayi nan zafi, wanda kan sanya ruwan jikin mutum saurin karewa ta hanyar zufa, dole mai azumi da fari sai ya guji rana. Muna ji a kafafen yada labarai yadda wasu har yawan wanka da jika jiki sukan yi domin sanyaya jiki saboda zafi. Wannan jika-jiki na daya daga cikin hanyoyin takaita karewar ruwa a jiki. Ga kuma wadanda za su iya, na’urar sanyaya wuri ma tana da irin wannan tasirin.Sannan da zarar an kai azumin bayan an tauna wani abu mai zaki(sukari) irinsu ‘ya’yan itatuwa sai a fara kokarin mai da ruwan jiki. Wasu sukan tambaya domin me a addinance ake farawa da dabino. Fa’idar dabino ita ce cewa shi yana da sinadaran suga kusan har nau’uka 4 (glucose, sucrose, fructose, da maltose) wadanda jiki ke bukata kuma wadanda za su fara aiki nan da nan ba sai jiki ya sarrafa ba. Har ila yau dabino yana da sinadarai irinsu potassium mai kara karfin mommotsa jiki da iron mai kara jini, da ma sauran sinadarai wadanda ba kasafai ake samun su a sauran ‘ya’yan itatuwa ba.

Wajen mai da ruwan jikin, shi gundarin abin bude-bakin zai fi kyau ya zamto mai ruwa-ruwa, duk wanda ran mutum ya ji ya fi bukata (mai sanyi ne ko mai zafi) dangane da yanayin da ake ciki. Abin da dai mutum ya ji zai iya sa hanjinsa su warware, ba wanda zai sa ciki ya yi kabe-kabe ba, ya cushe nan da nan, domin wasu kunu ko kamu ko shayi mai zafi ne ya fi warware masu hanji, kafin daga bisani su dora wani abu, wasu kuma abu mai sanyi ne ya fi warware masu hanji. Don haka sai mutum ya duba ya ga wane ne wanda in ya sha nan da nan zai ji ya bi jiki, bai zauna masa a ciki ba.

Ba dai aso a cika ciki tashi guda. Ba kuma a so a ci abinci dab da lokacin kwanciya.Can an jima idan aka zo cin abinci sosai, yana da kyau a kara yawan abinci masu gina jiki irinsu naman kifi ko na kaza ko na dabbar da aka samu, ko kwai da madara da awara da kosai da ire-irensu, gami da masu kara kuzari irinsu shinkafa da tuwo da burabusko da sauransu a iya ci daidai misali, fiye da sauran masu sa jiki tara kitse irinsu man shanu ko kakide ko bota.Idan aka yi sahur kuma kada a kwanta bayan Sallah kai tsaye har sai an kara awa daya zuwa biyu, ciki ya dan fada kafin a kwanta, domin kada mutum ya tashi da safe da kumburin ciki da kwarnafi.

 

Na gode da shawara game da yawan shan ruwan shayi domin tsakuwar kodata yanzu ta yi sauki. A yanzu akwai wasu shawarwari kuma dangane da watan Ramalan?

Daga Maman Abdul Gombe

Amsa: To madallah. Ga kuma shawarwari nan a sama dangane da cimakar Ramadan ga kowa da kowa.

 

Koshan ruwa mai sanyi daga kai azumi yana da wani alfanu kowata illa?

Daga Maryam Umar Katsina

Amsa: Ke ma da fatan kin karanta amsarki a bayani na sama. An ce ya danganta daga irin cikin mutum. Wasu sai sun sha mai sanyin ne suke jin dadin cikinsu da jikinsu, wasu kuma sai dai mai zafi, domin idan suka sha mai sanyi zai tsaitsaya masu su ji ciki ya tsaya kam.

 

Ni ma a wasu lokuta ko da ina jin yunwa ba na iya cin abinci mai nauyi irinsu shinkafa ko tuwo kai tsaye sai dai masu ruwa-ruwa kamar ‘ya’yan itatuwa. Ko hakan yana nufin alamun wata matsala ne?

Daga K. Bello Kiyawa

Amsa: A’a ba wata matsala in dai bayan ka sha abu mai ruwa-ruwa ko kayan itatuwan hanjin na warwarewa bayan wani lokaci ka dawo ka iya cin mai dan nauyin. Kuma da ma ai a tsarin cimaka a ko’ina a duniya idan ka je manya-manyan gidajen abinci inda ake da tsarin cimaka ukku (3-course meal) ba mai nauyi ake fara kawo maka ba, mai ruwa-ruwa ake fara kawowa, kayan shaye-shaye da suke kira soup, wato kamar wani romo ne ko farfesu ko ma kunu da za ka fara gasa ciki da warware hanji da shi kafin a kawo maka mai nauyi. Ka ga kenan ko kwararrun masu abinci sun san sai an fara ware hanji kafin a dora mai nauyi.

 

Kamar yadda aka yi bayani akwai wadanda ba sa iya daukar azumi, nima ina da ciwon cikin olsa wanda ko da azumi daya na yi idan ya tashi sai watan ya mutu ina kwance ba lafiya. To mu irinmu ya za mu yi?

Daga Jamilu, Gumel

Amsa: Ai an fadi amsar a bayanin. Aka ce su wadanda suke da rashin lafiya ai ba za su yi azumi ba a addinance da kuma a likitance. Ai ayar Al-Kur’ani ce ma sukutum ta dauke masu, sai dai su rama idan sun ji sauki ko su ciyar idan ba ranar warkewa. Kuma muka ce a samu a tuntubi Mallamai su yi maka karin bayani bayan ka je likita ya hanga cikin ya ga irin olsar da take ciki. Ka san wani lokaci ba olsa ba ne, amma da an haska da kyamara a asibiti ana iya ganin ko ma mene ne, a baka magani.

 

Wane irin abinci ne mai ciwon hanta ba zai iya ci ba?

Daga Shehu IBB Market

Amsa: Ita ma wannan tambayar kamar mun taba amsata. A ‘yan shekarun baya koyarwar ita ce kada mai ciwon hanta ya yawaita cin nau’in abinci mai gina jiki na protein, ya ci mai kara kuzari na carbohydrare amma a yanzu da yake aikin namu yana tafiya ta bincike, koyarwar ta canza, an ce zai iyacin duk abin da ya ga dama. Sai dai kawai mutum ya tabbatar an gano masa irin ciwon hantar tasa kuma yana karbar magani da shawarwari a wurin likitan kayan ciki wato GIT kwararre.

 

Ni idan na sha madara sai cikina ya rika ciwo. Ko me ya sa?

Daga Zakari Waziri, Lagos

Amsa: E, akwai mutanen da madara ba ta karbecsu ba. watakila kai ma kana cikinsu. Sai ka nemi sauyi zuwa madarar waken soya ka rika sha,domin ita ta fi karbar irin ku.

 

Shin gaskiya ne yawan shan kofi da gahwa kan iya sa kansa?

Daga Muhammad Goni, Yobe

Amsa: A’a ba gaskiya ba ne, sukan dai sa yawan karancin barci, da yawan fitsari, su kararwa mutum dan ruwan jikinsa, da kuma naci wato addiction, mutum ya ji idan ya saba sosai idan bai sha ba kamar ya mutu.