✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa soyayya ke komawa kiyayya, masoya ke zama abokan gaba? (2)

Yau ma fa FDK babu hutu, domin kuwa sakonni sai kwararowa suke zuwa komarsa. Shi kuwa ya mike daga kishinkida yana ta karantawa. Ko me…

Yau ma fa FDK babu hutu, domin kuwa sakonni sai kwararowa suke zuwa komarsa. Shi kuwa ya mike daga kishinkida yana ta karantawa. Ko me suke cewa dangane da wannan maudu’i, wanda ya zama ruwan dare game da duniya?

Sako na farko ya zo daga Musa G.G.C Kurna Kano (08038822292): “A gaskiya rashin rikon amana tun lokacin da ake zuwa zance, mazan karya, matan karya, sai daga karshe ido ya raina fata. Daya daga ciki ya nemi a rabu tunda dai asiri ya tonu. Yayin da shi kuma dayan zai ce zama daram. To fa komai zai iya faruwa, tunda dama su mata ba su cika daukar kaddara ba.”

Sai kuma Abdul Abdulhamid Zamfara (08167515363), wanda ke cewa: “Hakika akwai abubuwa da suke kawo kiyayya a bangaren soyayya ko kuma zamantakewar al’umma. Ko dai ya kasance saurayi ya nemi budurwa da zimmar su yi aure ta ki aminta ko ita budurwa ta nemi saurayi amma ya ki ta, daga karshe sai soyayya ta juye ta zama kiyayya.”

Shi kuwa Ahmad Ghali (09054986613) yana cewa: “FDK, abin da ke kawo yawaitar kashe-kashe da fadace-fadace da sauransu, a sanina shi ne, laifi ne da ya shafi kowa, maza da mata. Na farko shi ne karancin ilimi, rashin hakuri da juna. Ya kamata miji ya san da cewa mata suna da karamar kwakwalwa da karancin dogon tunani, wanda zai jawo mata abin da ba ta tunani; har daga baya tana da na sani. Lura da wannan, ya kamata mazan aure su kara hakuri da juna.”

Ita ma Hauwa Salihu Umar Jos, ba a bar ta baya ba, inda take cewa: “A gaskiya ni a ganina rashin gina so a tafarkin gaskiya, shi yake jawo haka. In har saurayi yana yi wa budurwa karya idan ta gane dole ta koma kiyayya.”

Sako ya zo daga Barrister Umar (07034497275) yana cewa: “FDK, ina matukar farin ciki da jin dadin ganin wannan maudu’i. Gani nake kamar ni ake tambaya, ganin abin ya faru da ni. Abin da ya sa soyayyarmu ta koma kiyayya shi ne, da farko tunda muka fara soyayya ba na kwana uku ban kira ta ba amma ba ta taba kirana ba, ban mata magana ba sannan abin da ya sa soyayyarmu ta zama kiyayya; idan na zo zance, muna cikin hira sai ta ce mini ana kiranta a gida. Ashe wajen wani saurayin take tafiya kuma da na gane haka sai na nuna mata wannan bai kamata ba, ba ya cikin tsarin soyayya. Ta ki dainawa, ni kuma abin yana bata min rai sosai, na kasa hakura kuma ta ki fada min ba ta sona. Daga karshe da na yi mata magana sai ta nuna min ba ta so wai mutum ya zo ta ki zuwa. Ni kuma na ki hakura, a karshe dai yanzu ba mu magana da ita kusan wata uku kuma kullum muna tare da ita. A karshe dai zan ce muku Allah Ya ba mu mace tagari.”

Daga Aminu Isyaku KFR (07088359743): “Babbar magana! A gaskiya FDK ka kawo maudu’i mai matukar muhimmanci. Ni a ra’ayina hakan yana faruwa ne daga mu maza saboda yawancinmu muna yi wa mata karyar kudi koda ta magana ce, ka ji mutum yana cewa yana da kaza da kaza, alhalin ba shi da shi. Su kuma mata ga kwadayi, in ba ka yi musu karyar ba ba za ku daidaita ba. Don haka dole a samu matsala, so ya zama gaba kuma da rashin hakuri a bangaren maza da mata. Don haka ina ganin kawai soyayyar karya ce ke kawo wannan matsalar, sai mun gyara sannan a samu maslaha.”

Sai kuma Nura Mai Apple Gusau (08133376020), wanda ya bayyana cewa: “Haƙika babban abin da yake janyo soyayya ta koma ƙiyayya shi ne, dukkan abin da ba a tsara shi kan gaskiya ba tunda farko, to a ƙarshe ba ya kyau.  Mafi yawa daga cikin waɗanda irin wannan hali ya fi shafa su ne masoyan juna a zahiri, waɗanda suka tsara soyayyar ƙarya don yaudara saboda son cimma wata manufa ta daban. Babu shakka duk lokacin da aka samu rarrabuwar kai, to ƙiyayyar da za ta biyo baya za ta zama ina ma ba a taɓa sanin juna ba. Allah Ya kyauta kuma Ya bar mu da masoyanmu na gaskiya.”

Sadik J.M.T Suleja (07012115752): “FDK, mun gode da wannan sabon maudu’i, inda yake cewa me ya sa soyayya ke komawa kiyayya, masoya ke komawa abokan gaba? To, hasali dai jigonsu duka shi ne rashin hakuri.

“Masoya: Wadansu ba su yi don Allah. To, dama duk abin da za a yi ba don Allah ba ba a kaiwa gaci. Saurayi zai zo ya samu budurwa ya nuna yana sonta ko kuma ita budurwar ta samu saurayi a kan tana sonsa, sai duk su amince amma ba a tunanin cewa shin ra’ayi ya zo daya, don Allah aka yi ko akasin haka? Sai an yi nisa sai a fahimci dama yaudara ce, sai tarwatsewa.

“Ma’aurata: A yi karya a zo gida a ga kuma ba haka ba ne, rashin girmama juna, daukar zantuka daga mugayen kawaye, karo mata kishiya to fa nan ne ake samun babbar matsala. Za a fara habaici da zage-zage, nan ne ake samun mace ta watsa wa mijin ruwan zafi, nan ne mace take daukar alwashin kisa; har ma a kai ga kisan.

“Iyaye: Auren dole na taka gagarumar rawa wajen wadanda aka yi wa auren dole su koma makiyan juna da gaba tsakanisu.

“Abokai: Daukar maganganu marasa tushe balle makama daga munafikai. Shi munafiki zai zo ya bata wancan a wurin wannan, ya koma gun wancan ya bata wancan din a wajensa, sai sun hadu a rika yi wa juna kallon hadarin kaji. Karshe dai ma’aikata ne za su raba su.

“Kawaye: Su ma dai irin abokai ne, su kuma munafika ce take raba su. Babban abu dai shi ne, rashin hakuri. Fatanmu dai Ubangiji Sarki Allah Ya tsare mu daga sharrin Shaidan jefaffe daga rahamar Allah, amin.”