Da Dumi Dumi

Me ya sa soyayya ke komawa kiyayya, masoya ke zama abokan gaba? (5)

Babu mai cin zarafin mace sai sakaran namiji!
Babu mai cin zarafin mace sai sakaran namiji!

Ya ’yan uwa masu bibiyar wannan muhimmin shafin na Dausayin Kauna, a farfajiyar FDK! Ina yi muku gaisuwar Barka da Sallah, duk da cewa mun kwana biyu da wannan muhimmin shagali A yau mun shiga mako na biyar a wannan maudu’i da ke bin kadin yadda al’amuran soyayya ke rikidewa gaba a tsakanin masoya maza da mata.  Ga sakonnin da suka samu shiga a wannan makon, sai a ci gaba da bibiyarmu da hakuri:

Wani mutum wanda bai rubuto sunansa da lambarsa ba, ya bude maudu’in namu da cewa: “A ciki akwai masu ganin rashin ilimi ne ke haddasa haka. To, ni ban yi gardama ba, amma da zamaninmu na yanzu da na iyayenmu wanne ya fi ilimi? Ga masu cewa auren dole kuwa, su tuna cewa a da ma ana hada auren dole kuma ba a samun kiyayya. Ni dai na fi ganin cewa ana gina rayuwa da haramun, inda saboda haka sai a samu yaran da ba su da tarbiyya, domin abincin da aka ci aka same su haramun ne kuma da haramun aka ciyar da su har suka girma. Dalili ke nan ake samun yaran yanzu maza da mata babu tarbiyya, babu soyayyar juna sai mugunta da kaushin zuciya. Dalili ke nan da zarar sun samu sabani sai su fara aiwatar da abin da bai dace ba, na kashe-kashen juna da sauransu. Allah Ya kyauta, amin.”

Imrana Abdullahi Abuja (09018601318): “Assalamu alaikum wa rahmatullah. A gaskiya ni dai a ganina, duk lokacin da haka ta kasance, to za ka ga wannan masoyan ba su gina soyayyar gaskiya ba. Amma idan mutum ya gina abin gaskiya, to haka ba za ta faru ba. Ya Allah Ka sa mu gina soyayyar gaskiya don cin moriyarta.”

Daga Baban Soyayya, ya aiko sakonsa, inda yake cewa: “Na karanta sakonka a jarida kuma hakan gaskiya ne, soyayya tana komawa kiyayya; domin ni ma kafin in samu wannan matsayi na Baban Soyayya na sha wuya sosai.”

Daga Imam Suraj Tafoki Faskari, Jihar Katsina, Mazaunin Abuja Gwarinpa (09063465221): “Assalamu alaikum warahamatullah. Malam FDK, ina yi maka barka da zagayowar Babbar Sallah, kai da sauran masu bibiyar wannan shafin. Malam, don Allah ka sa min cigiyar kanwata kuma masoyiyata. Ita ce Nauwara A. Mu’alliyat, Sharada Kano. Ka ce mata yayanta kuma masoyinta Imam yana cikin magagin kaunarta, ina sauraren kiranta a koyaushe. Ka huta lafiya.”

ADVERTISEMENT

Daga Idris One in Town Gombe: “Assalamu alaikum. Ina yi wa dukkan ’yan uwa Musulmi Barka da Sallah. Allah Ubangiji Ya maimaita mana ta badin badada.”

Sako daga Ahmed Kudi Masussuka (08081266888), yana cewa: “A gaskiya FDK abin da ke sa soyayya ke zama gaba, ba wani abu ba ne illa rashin hakuri da juna.”

Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688): “Duk da na san cewa akwai farin ciki a soyayya fiye da bacin rai, amma zan iya cewa na huta da ba-ni-ba-ni, domin ba ni da budurwa a yanzu. Hankali kwance Sallah ta zo, ba wacce na yi wa dinki ko na hada wa kayan kwalliya. ’Yan uwana samari a kiyayi yin budurwa Ranar Sallah, ta haka ne kawai za a kauce wa zaben tumun dare. Ina yi wa daukacin mabiya wannan shafi fatar alheri. Da fatar an yi bukukuwan Sallah lafiya.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya