✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa soyayya ke komawa kiyayya, masoya ke zama abokan gaba?

Ooo ni FDK! Ina kishingide a cikin lambuna, wata iska mai sanyi na ratsa ni. A gefe daya akwatin rediyona na ta amayar da labarai…

Ooo ni FDK! Ina kishingide a cikin lambuna, wata iska mai sanyi na ratsa ni. A gefe daya akwatin rediyona na ta amayar da labarai iri daban-daban, sai wani rahoto ya dauki hankalina, yadda aka ce a cikin mako daya, an samu matan aure sama da uku sun kashe mazansu, wata kuma ta kwara wa nata mijin tafasasshen ruwa a gabansa, wai saboda zai kara aure. Na kidime da tunani, cewa a lokuta da dama fa ma’auratan nan suna zaune da juna cikin kauna da soyayyar juna, ta amma me zai sanya a wayi gari su koma makiya kuma abokan gabar juna? Ba a aure kadai hakan ke faruwa ba, ana samun haka a zamantakewar al’umma. Abin tambayar shi ne, wadanne dalilai ne ke haddasa irin wannan yanayi? Mutane da yawan gaske sun aiko da ra’ayoyinsu dangane da wannan maudu’i, ga kadan daga abin da suke cewa:

Abdullahi A. Skuare Akure: “A gaskiyar magana, abin da yake kawo mata ke kashe mazansu shi ne auren dole kuma a gaskiya akwai laifinmu. Mu samarin za ka ga saurayi mace ta ce ba ta son sa amma ya nace sai ya aure ta. Wata ma har kirari za ka ji ta yi masa, cewa idan aka daura auren za ta kashe shi amma ya ki saurare!”

Amiru Isa, Tashar Guga, Bakori (07068147933): “FDK, akwai dalilai da dama masu maida soyaya zama kiyayya, har masoya su zama abokan gaba. Talauci, yawan tambayar kudi kuma ya kasance babu. Ita za ta yi zaton yana da su hana ta ya yi. Rashin ilimi, idan akwai jahilci tattare da masoya, lokaci kadan soyayyarsu ke zama kiyayya. Tilasta wa masoyi yin abin da bai da niyya. FDK, ni shaida ne, na nemi aure an kusa daurawa, da yake ’yar wahala ce sai ta ce in yarda duk mako zan rika zuba mata adashin N1,000. Na ga ban iyawa, ni ba sakarai ba ne sai na kiyaye ta. Yanzu ko ganinta ban son yi. Yaudarar juna, kin tsayawa kan soyayyar gaskiya, daukar gulma, wulakanta iyayen juna, kin biyan bashin juna, rashin biyayya, jefa wa juna kalaman batanci, rashin cika alkawari, zagin juna, sata, cin mutuncin juna, duka da rashin abinci ko rashin sutura; duk wadannan na taimakawa wajen mai da soyayya zama kiyayya.”

Y.Y. Dantsoho Kaduna: “FDK, idan muka dubi yadda ake gina soyayya har a yi aure a da da yanzu, dole a rika samun nakasu. Iyaye a baya, mutunci suke dubawa sannan yaransu su ginu a kan haka, a yi aure a kuma zauna lafiya. Yanzu kuwa mafi yawancin iyaye da yaransu wadata, matsayi ko wani abu mai dushewa suke la’akari da shi. Ka ga ke nan dole kiyayya ta biyo baya. Ga zamantakewa kuwa ya kasance aibu, kasawa da gurgunta junanmu shi aka sa gaba a yau, ba yarda da juna, ba kauna, ba zumunci, sai cin dunduniya. Ka ga ke nan al’amarin jituwa zai yi wuya. Mata masu kisan mazansu kuma don dalilai masu rauni, Allah na jiransu, ganin cewa babu Shari’ar Musulunci da za ta yi maganin lamarin.”

Rabilu Sulaiman Lawan Benin City (08147343734): “FDK, ni a ganina, mafi yawancin soyayyar ce ba a gina ta da gaskiya ba, an gina ta ce don kwadayin wani abu a tsakanin masoyan.”

Umar Abubakar Jos (08146008166): “Kadan daga cikin abin da ke haddasa hakan, na forko akwai ba da soyayya wadda ta wuce gona da iri. Annbi Muhammad (SAW) ya ce idan za ka so, ka yi sesa-sesa, idan za ka ki, ka ki sesa-sesa, watakila wata rana makiyinka na iya zama msoyinka, masoyinka kuma na iya zama makiyinka.”

Gimbiya Asma’u Kano: “FDK, an ce ‘zo mu zauna, zo mu saba’ kuma ‘masoyi kan zama makiyi, makiyi kuma masoyi.’ Karya da wadansu maza ke yi da kuma mata masu kwadayi wadanda sai da karyar maza ke samun kansu, yakan jawo hakan da kuma da-na-sani a batun soyayyar. A zamantakewa kuwa, yau ba mu kaunar junanmu, sai hassada da sauransu. Ka ga ke nan sai a hankali. Mata masu kashe mazansu kuwa, a yi masu hukuncin da shari’a ta tanadar kawai.”

A’isha A. Saeed Katsina (08133548668): “FDK, wannan kuma wani yanayi ne na daban da yake faruwa tsakanin masoya, wani lokacin kuma har ga ma’aurata. Fatanmu dai Allah Ya shige mana gaba.”

Dahiru Dauda (KGY) Bindawa (08030693021): “Biyu daga cikin dalilan da suke haddasa irin wannan mummunan yanayi, su ne kuskurenmu wajen gina soyayya ba tare da kyakkyawan sanin juna tare da kyakkyawar fahimtar juna ba. Sai kuma haduwar hudubar Shaidan da rashin tarbiyya, tare da raunin imani ai’nun; duk a wuri daya su ke haddasa wannan, a fahimtata. Allah Ya ganar da mu, amin.”