✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me za a ba yara su taka da wuri?

Akwai maganin da za a iya ba yara domin su samu takawa da sauri? Daga Maman Walid Amsa: Kwarai kuwa akwai. Amma kafin a je…

Akwai maganin da za a iya ba yara domin su samu takawa da sauri?

Daga Maman Walid

Amsa: Kwarai kuwa akwai. Amma kafin a je ga magani, ai akwai maganin a abincinmu. Sinadaran calcium da na bitamin na rukunin D su ne sirrin takawar yara da wuri, domin su suke sa kwarin kashi. Su ake ba yara domin kasusuwansu su yi kwari domin su yi saurin takawa. Kuma ana samunsu a abinci irinsu kifi da kwai da madara da hanta da man ja. Don haka idan kina yawan ba yaran naki wadannan shi ke nan ba sai an nemi magani ba, Idan kuma ba za a iya jure sayen irin wadannan abinci kullum ba ko idan yaron bai cika karbar abinci ba, shi ne sai an kara da magani. Abubuwan da ke cikin maganin kara kwarin kashi a yara su ne dai sinadaran calcium da bitamin na D. Sai ki auna ki gani abinci ne ya fi araha ko magunguna. Sa’annan a yara masu shan mama, ita kanta uwa ita za ta nemi wadannan nau’ukan abinci ta rika ci da sha domin yaron ya samu a mama ya sha. Duk da haka akwai wasu likitocin yara da suke ganin ko da tana ci a abinci, idan mace na shayarwa za ta iya sayen sinadaran calcium da na bitaman na rukunin D a irin na cikin multibite a kyamis, ta sha domin ita da jaririnta da take shayarwa tunda suna ganin sinadaran na cikin abinci kadai ba zai ishesu su biyu ba, ko ma su uku idan tagwaye ne ‘ya’yan ko ma abin da ya haura haka. Wato idan tagwaye ne ko abin da ya haura biyu dole ne ba sai ta kara da wadannan multibite din abin zai isa.

Yawan shan ruwan sanyi na kankara ga mata masu juna biyu ko shin akwai wata matsala da hakan kan iya haifarwa

Daga Ali Fancy, Garko

Amsa: A’a a likitance mu ba wata matsala ga jariri idan mace tana shan ruwan sanyi, tunda ba jinjirin da ke ciki take kwarawa ruwan sanyin ba, domin abin da ma yake kawo wannan rashin fahimta kenan, sai a dauka idan mace ta sha ruwan sanyi ai ruwan sanyin kan jariri zai zuba. A’a ba haka abin yake ba, ciki daban mahaifa daban, wato jariri na nan nade a cikin mahaifa a ciki, ba ma a kusa da inda ake zuba abinci yake ba, a mara yake, sai cikin ya girma ne yakan iya kusantar tumbin da ake zuba tuwo.