Search
Subscribe
Mercy Johnson-Okojie ta zama Jakadiyar madarar Hollandia

Mercy Johnson-Okojie

Mercy Johnson-Okojie ta zama Jakadiyar madarar Hollandia

Kamfanin madarar Hollandia da ke sahun gaba wajen hada madarar gwangwani da yugot a Najeriya, ya bayyana nada Mercy Johnson-Okojie, a matsayin sabuwar Jakadiyar Madarar Hollandia. Jarumar wadda  ta yi fice a harkar fina-finan Najeriya kuma matar aure uwa. Mercy Johnson-Okojie, ta zama wacce ake tallatawa a dukkan madarar da kamfanin yake sana’antawa.

Wannan hadin gwiwar dai zai ba ta damar tallatawa tare bayyana yadda kamfanin ya zama silar cimma muradunta daban-daban a rayuwa. Yayin da za ta bukaci kwastomomi ma da su yi haka.  Nasarar da Mercy ta samu ya nuna karara irin tarin basira da fikirar da take da su.

Madarar Hollandia Ebap tana da zaki da gardi da kuma dadin dandano da ta yi daidai da abinci da kuma tande-tande.  Ana sa ran Mercy za ta yi aiki da hazakarta wajen tallata amfanin da ke tattare da madarar Hollandia Ebap ta yadda za ta gamsar da jama’a su saya.

Manajan Daraktan Kamfanin Chi. Mista Deepanjan Roy ya bayyana cewa kokarinta a fili yake kan dukkan abin da take yi kuma tana da dukkan abin da ake bukata wajen tallata madarar.

“Mun zabi Mercy Johnson-Okojie, don ta zama abar tallata madararmu ta Hollandia Ebap, sakamakon imanin da muka yi na za ta iya kara daga kimar madarar a idon kowa kuma ta gamsar da mutum wajen sayen madarar. Muna farin ciki sosai da ta kasance Jakadiyar Hollandia Ebap,” inji shi.

Ana sayar da madarar Hollandia a cikin yanayi mai tsabta. Jakar ledar madarar na samuwa  a nauyin giram 90 da 120 da  190. Kuma ana iya samun madarar a kanana da manyan shagunan Chi Shoppes da kanana da manyan shaguna a duk fadin Najeriya.   Buhun masara 8 na fara nomawa amma yanzu ina noma buhu 8,000 – Kamilu Sigau

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin