Search
Subscribe
Messi ne ya aika wa Neymar sakon tes don ya koma Barcelona

Messi ne ya aika wa Neymar sakon tes don ya koma Barcelona

 

Rahoton da kafar labarai ta Mailonline ta kalato ya nun cewa dan kwallon FC Barcelona, Lionel Messi ne ya aika wa Neymar sakon tes a asirce don ya sake komawa FC Barcelona kafin a rufe kakar wasa a ranar Litinin.

Bincike ya nuna sakon ne ya tunzura Neymar wajen  yi wa PSG bore don su sayar da shi ko ta halin kaka kafin a rufe kasuwar sayar da ’yan kwallon.

Sai dai da kulob din PSG ya fuskanci inda Neymar ya dosa ne sai ya cika masa kudi inda ya nemi duk kulob din da ke bukatarsa sai ya ajiye Fam miliyan 273 (kimanin Naira tiriliyan 1 da biliyan 203 da miliyan 90) kafin  sayar da shi.

Saboda karancin kudi ya sa Barcelona ta hada ’yan kwallonta uku ciki har da Iban Rakitic da Osumane Dambele da kuma Fam miliyan 120 a cinikin amma  kulob din PSG ya ki amincewa har aka rufe kasuwar sayar da ’yan kwallon a ranar Litinin da ta wuce.

Yanzu dai Neymar zai ci gaba da zama a PSG har sai abin da hali ya yi.

Kimanin shekara uku ke nan da Neymar ya canja sheka daga Barcelona zuwa PSG a kan Yuro miliyan 222 (kimanin Naira biliyan 876).

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin