Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Messi ya gamu da fushin ’yan Barcelona

Shahararren dan kwallon FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya gamu da fushin wadansu daga cikin magoya bayan kulob din jim kadan bayan an tashi wasa a tsakanin Liberpool da ke Ingila da FC Barcelona na Sifen a ranar Talatar da ta wuce a gasar Zakarun Turai a matakin semi-fainal.

A wasan, Liberpool ce ta lallasa FC Barcelona da ci 4-0, jimilla 4-3 wanda hakan ya sa Liberpool ta kai wasan karshe.

ADVERTISEMENT

Sakamakon ya bakanta ran da yawa daga cikin magoya bayan Barcelona, abin da ya sa wadansu daga ciki suka rika zagin Messi a filin jirgin sama lokacin da ’yan kwallon suke kokarin komawa Sifen.

 

ADVERTISEMENT