✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya kafa sabon tarihi a FC Barcelona

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din FC Barcelona na Sifen sun ce shahararren dan kwallon kulob din, Lionel Messi ya kafa sabon tarihi a…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din FC Barcelona na Sifen sun ce shahararren dan kwallon kulob din, Lionel Messi ya kafa sabon tarihi a kulob din a ranar Asabar da ta wuce bayan ya lashe Kofin La-Liga har sau takwas.

Kulob din Barcelona ya lashe Kofin La-Liga sau 8 a tsakanin shekara 11.

Hakan ya sa Messi ya lashe wannan gasa fiye da kowane dan kwallo a FC Barcelona kawo yanzu.

Hatta Andre Iniesta, tsohon dan kwallon kulob din bai kama kafar Messi a yawan lashe kofin La-Liga ba.

Messi ne ya zura kwallo daya tilo a ragar Lebante a ranar Asabar da ta wuce bayan ya canja Philip Coutinho jim kadan da komawa hutun rabin lokaci da hakan ya sa aka tashi wasan ci 1-0.  Wannan nasara ce ta ba FC Barcelona damar lashe gasar ta bana duk da ana saura wasanni biyu a kammala gasar.