Aminiya

Messi ya kafa sabon tarihi a La-Liga

Dan kwallon FC Barcelona na Spain, Lionel Messi, ya sake kafa sabon tarihi a  Gasar La-Liga ta Spain bayan da ya zura kwallo a ragar Sebilla a bugun tazara.  Wannan kwallo ta kasance ta 420 a wasanni 455 da ya yi a gasar.

Barcelona ta zura kwallaye 4-0 ne a ragar Sebilla a ranar Lahadin da ta wuce.

ADVERTISEMENT

Yanzu Messi  ya doke abokin takararsa Cristiano Ronaldo da ke da yawan kwallaye 419.

Ana duba ’yan kwallon da suka fi yawan zura kwallaye ne a gasanni biyar a Turai da suka hada da Firimiya a Ingila da La-Liga a Spain da Serie A a Italiya da Ligue 1 a Faransa da kuma  Bundesliga a Jamus inda yanzu Messi ya kasance na daya.

ADVERTISEMENT

Sai dai Ronaldo da ke da yawan kwallaye 419 ya same su ne a gasanni daban-daban da suka hada da kwallaye 84 a kulob din Manchester United na Ingila da kwallaye 311 a kulob din Real Madrid na Spain da kuma kwallaye 24 a kulob dinsa na yanzu wato Jubentus na Italiya.

Sai dai komai zai iya faruwa a tsakanin Messi da Ronaldo ganin an shiga kaka ta bana kuma akwai yiwuwar ’yan kwallon za su ci gaba da zura kwallaye a raga.