✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya lashe kyautar takalmin zinare a karo na 5

Kyaftin din kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya sake lashe kyautar takalmin zinare a karo na 5 bayan ya kasance dan kwallon da…

Kyaftin din kulob din FC Barcelona da ke Sifen ya sake lashe kyautar takalmin zinare a karo na 5 bayan ya kasance dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye a raga a kakar wasa ta 2017/2018.

A ranar Litinin da ta wuce ce Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai ta zabe shi a matsayin dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye a Nahiyar Turai a kakar wasan da ta wuce.

Messi ya samu nasarar ce bayan ya zura kwallaye 34 a gasar La-Liga ta Sifen da hakan ya sa kulob din Barcelona ya zama zakara. Sannan dan kwallon Liberpool Mohammed Salah ne ya zama na biyu bayan ya zura kwallaye 32 a raga a gasar Firimiya ta Ingila.

Messi da suke kankankan da Cristiano Ronaldo wajen lashe wannan kyauta sau hur-hudu, yanzu ya shiga gaban Ronaldo bayan ya lashe ta biyar a bana.

A shekarar 2009/2010 ne Messi ya lashe ta farko bayan ya zura kwallaye 34 a raga sai a 2011/ 2012  ya lashe bayan ya zura kwallaye 50.  A 2012/ 2013 ya lashe ta uku bayan ya zura kwallaye 46 a raga yayin da ya sake lashewa a 2016/2017.  Sai a bana da ya sake lashe ta biyar bayan ya zura kwallaye 34 a raga.

A kakar wasa ta bana ma Messi ne yake kan gaba wajen yawan zura kwallaye a raga, inda ya zura ta 14 a ranar Lahadin da ta wuce.

Kawo yanzu Messi ne ya fi yawan zura a kulob din FC Barcelona, inda ya yi mata wasanni 655 kuma ya zura kwallaye 572 a raga.