Da Dumi Dumi

Messi ya musanta cewa zai fitar da Ronaldhinho daga kurukuku

Shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi ya musanta jita-jitar da ake bazawa cewa zai fitar da tsohon dan kwallon Brazil da suka yi wasa tare a kulob din FC Barcelona na Spain Ronaldhinho daga gidan yari.

Ronaldhinho mai shekara 39 yanzu haka yana tsare ne a wani gidan yari a Paraguay tare da ’yan uwansa bisa zargin shiga kasar da fasfo na jabu. Idan an same su da laifi za a iya yanke musu hukuncin daurin wata shida.

Messi ya musanta wannan jita-jitar ce ta bakin lauyansa. Ya ce ko shakka babu yana tausayin Ronaldhinho game da mawuyacin halin da ya tsinci kansa a ciki a Paraguay, amma batun zai yi amfani da makudan kudi wajen kubutar da shi daga tuhumar da ake yi masa a Paraguay ba gaskiya ba ne.

An yi ta rade-radin Messi zai kashe kimanin Fam miliyan 3 (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 400) wajen daukar lauyoyin da za su kare Ronaldhinho daga tuhumar da ake yi masa a Paraguay batun da Messi ya musanta a ranar Talata.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya