✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya musanta cewa zai fitar da Ronaldhinho daga kurukuku

Shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi ya musanta jita-jitar da ake bazawa cewa zai fitar da tsohon dan kwallon Brazil da suka yi wasa tare…

Shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi ya musanta jita-jitar da ake bazawa cewa zai fitar da tsohon dan kwallon Brazil da suka yi wasa tare a kulob din FC Barcelona na Spain Ronaldhinho daga gidan yari.

Ronaldhinho mai shekara 39 yanzu haka yana tsare ne a wani gidan yari a Paraguay tare da ’yan uwansa bisa zargin shiga kasar da fasfo na jabu. Idan an same su da laifi za a iya yanke musu hukuncin daurin wata shida.

Messi ya musanta wannan jita-jitar ce ta bakin lauyansa. Ya ce ko shakka babu yana tausayin Ronaldhinho game da mawuyacin halin da ya tsinci kansa a ciki a Paraguay, amma batun zai yi amfani da makudan kudi wajen kubutar da shi daga tuhumar da ake yi masa a Paraguay ba gaskiya ba ne.

An yi ta rade-radin Messi zai kashe kimanin Fam miliyan 3 (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 400) wajen daukar lauyoyin da za su kare Ronaldhinho daga tuhumar da ake yi masa a Paraguay batun da Messi ya musanta a ranar Talata.