✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya zama Zakaran Kwallo na Duniya karo na 6

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana Lionel Messi na kasar Ajantina kuma dan kwallon FC Barcelona…

A ranar Litinin da ta wuce ne Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana Lionel Messi na kasar Ajantina kuma dan kwallon FC Barcelona da ke Spain a matsayin wanda ya lashe kambin Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya ta bana.

Messi ya lashe kambin ne bayan ya doke abokan takararsa, Birgil Ban Dijk dan kwallon Liberpool da ke Ingila da Cristiano Ronaldo dan kwallon Jubentus na Italiya da suka yi kan-kan-kan wajen lashe wannan gasa sau biyar-biyar.

Messi ya lashe kambin ne bayan ya samu kashi 55 daga cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada yayin da Ban Dijk ya samu kashi 24 daga cikin 100 sai Ronaldo ya samu kashi 21 daga cikin 100.

An zabi Messi ne saboda ya zura kwallaye 36 a raga a wasa 34 da ya yi a bara.  Sannan ya daga Kofin La-Liga na Spain.

Messi ya lashe kambin a shekarun  2009 da 2010 da 2011 da 2012 da 2015 da kuma 2019.

Sai dai wadansu masoya kwallon kafa suna ganin Messi bai cancanci lashe kambin na bana ba, ganin babu kofin da ya daga in ban da na La-Liga.  Yayin da Ban Dijk ya daga Kofin Zakarun Turai a karon farko, shi kuma Ronaldo ya lashe kofuna uku a bara.