Da Dumi Dumi

Michael ya mutu yana gab da samun makudan kudi – Bincike

Marigayi Michael JacksonBinciken kamfanin dillancin labarai na AP ya gano cewa, a lokacin da Micahel Jackson ke gab da mutuwa, a lokacin da yake shirye-shiryen gabatar da wani kwarya-kwaryan wasa a birnin Las begas, da zai dawo masa da martabarsa ta shahararren mawakin duniya, da ya samu gudanar da wasan, da ya samu zunzurutun kudi har Dala biliyan daya da rabi.
A Litinin da ta gabata ne wani kwararre ta fuskar kididdiga, Arthur Erk ya shaida haka a gaban kotu. Ya kara da cewa, baicin mutuwa ta iske mawakin, da ya samu nasarar gudanar da yawon wasannin da ya shirya, kuma ya mayar da hankali wajen kara wa tikintin wasan nasa daraja, babu shakka da ya samu wadannan zunzurutun kudi har ma da doriya.
Masanin ya ce, a kididdigarsa, da Michael ya samu gudanar da wannan wasa, da zai tattara kaddarori da la’ada daga kamfanoni daban-daban, kasancewar an kiyasta zai gudanar da wasanni 260 a sassa daba-daban na duniya.
Ta Allah ta kasance ne a kan mawaki Michael Jackson, shekaru hudu da suka gabata. Bai samu damar warkewa daga jinyar da ya kwanta ba, wadda ta hana shi sukunin gudanar da wannan gagarumin wasa da ya dade yana atisayensa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya