✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mikel Obi da bictor Moses na daga cikin ’yan kwallon da za su fafata a Gwarzon dan kwallon Afirka Na BBC

A ranar Litinin da ta wuce ne kafar sadarwar BBC ya fitar da sunayen ’yan kwallo biyar da za su fafafata a Gwarzon dan kwallon…

A ranar Litinin da ta wuce ne kafar sadarwar BBC ya fitar da sunayen ’yan kwallo biyar da za su fafafata a Gwarzon dan kwallon Afirka na bana.

‘Yan kwallo biyar ne kafar sadarwar ta zakulo ciki har da ’yan Najeriya biyu watau John Mikel Obi da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Chelsea na Ingila da kuma bictor Moses da ke buga kwallo a matsayin aro a kulob din Liberpool da ke Ingila.
Sauran ’yan kwallo ukun da za su fafata a gasar sun hada da dan Burkina Faso mai suna Jonathan Pitroipa da ke buga kwallo a kulob din Rennes da ke Faransa da Pierre-Emerick Aubameyang dan Gabon da ke buga wa kulob din Borussia Dortmund ta Jamus kwallo da kuma dan kasar Kwaddebuwa Yaya Toure da yanzu haka yake kwallo a kulob din Manchester City na Ingila. Wannan shi ne karo na biyar da Yaya Toure yake fafatawa a wannan gasa.
A ranar 25 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa da ke daukacin Nahiyar Afirka za su kada kuri’a don zabar Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana sannna a ranar 2 ga watan Disamban, 2013 ne ake sa ran za a fitar da sakamakon wanda ya lashe a shirye-shiryen da gidan Rediyo da Talabijin na BBC zai gabatar da misalin karfe bakwai saura minti 25 na dare agogon Najeriya.