Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mikel Obi ya bude cibiyar horar da yara kwallo a Legas

Mikel Obi da baqar riga tare da waxansu daga cikin yaran da cibiyarsa za ta fara horar da su qwallon qafa da ya buxe a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ce shahararren dan kwallon Najeriya John Mikel Obi ya bude wata cibiyar horar da yara ’yan shekara 3 zuwa 15 kwallo a Jihar Legas.

Cibiyar wacce ya bude a Children International School da ke Lekki a Legas, tun a shekarar 2012 ya samar da ita  amma sai a ranar Lahadin da ta wuce aka yi bikin bude ta.

ADVERTISEMENT

Kafar labarai ta Pulse ta ruwaito cewa yanzu haka cibiyar ta dauki yara da shekarunsa suka kama daga 3 zuwa 15 su 150 don horar da su kwallon kafa a kashin farko inda ake sa ran nan gaba kadan za a sake dibar wadansu don a ci gaba da horar da su yadda ake wasan kwallon kafa.

Rahoton ya ce, Obi ya yanke shawarar bude cibiyar ce don ya bayar da tasa gudunmawa a bangaren kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya musamman ganin shi ma ya fara kwallonsa ne a lokacin da yake matashi a irin wannan cibiya.

ADVERTISEMENT

Dan kimanin shekara 31, Mikel Obi da yanzu haka shi ne Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, ya taba buga wa kulob din Chelsea na Ingila wasa kafin ya canja sheka zuwa kulob din Tianjin TEDA na Rasha.  Ya samu nasarar lashe manyan kofuna a fagen kwallon kafa musamman a lokacin da yake Ingila.

“Na yanke shawarar kafa wannan cibiya ce don zakulo hazikan ’yan kwallo tun suna kanana. Kuma cibiyar za ta rika zakulo hazikan ’yan kwallo ne a ciki da wajen Najeriya, inda za a rika horar da su harkar kwallo kai-tsaye daga wajen kwararru da hakan zai sa a amfana da su a ciki da wajen Najeriya,” inji shi.

Cibiyar za ta killace yaran ne ana kula da cinsu da shansu da ba su wajen kwana.  Sannan za a rika gayyato kwararrun masu horar da kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya don koya musu kwallon kafa ta hanyar horar da su a aji da filin kwallo. Idan sun kware sai cibiyar da rika sayar da su ga duk kulob din da ke bukatarsu a ciki da wajen Najeriya.

Masana harkar kwallo sun yaba wa Obi a kan wannan tunani da ya yi na bunkasa harkar kwallon kafa ba a Najeriya kadai ba, a daukacin Afirka da duniya baki daya.

Tuni yaran da aka diba a cibiyar suka fara samun horo, kuma ana sa ran nan gaba kadan za a fara cin gajiyarsu a kulob-kulob da ke ciki da kuma wajen Najeriya, musamman matasan da shekarunsu suka kai 15.